Tashin Fetur: Ana son Bata Sunan Tinubu – Sheikh Jingir

 

Jihar Plateau – Shugaban kungiyar Izala mai hedikwata a jihar Filato ya yi kira ga shugaba Bola Tinubu kan tausayawa talakawa.

Sheikh Muhammadu Sani Yahaya Jingir ya yi magana ne kan karin kudin man fetur da aka yi a Najeriya.

Legit ta tatttaro abin da Sheikh Jingir ya fada ne a cikin wani bidiyo da Hamza Muhammad Sani ya wallafa a Facebook.

Ana son bata sunan Tinubu inji Jingir

Sheikh Muhammadu Sani Yahaya Jingir ya ce makiya tikitin Musulmi da Musulmi ne suka kara kudin man fetur.

Malamin ya ce sun kara kudin man fetur ne domin shafawa Bola Ahmed Tinubu kashin kaji a idon Musulmi masu son shi.

Ya ce saboda haka ne sai da suka bari shugaba Bola Tinubu ya tafi kasar Sin domin ayyuka na musamman suka kara kudin man fetur.

Jingir ya ce Tinubu zai saukakawa talaka

Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce yana da tabbas shugaban kasa Bola Tinubu zai ji koken talakawa idan ya dawo gida Najeriya.

Malamin ya ce ya fadi haka ne saboda Bola Ahmed Tinubu yana sauraron jama’a a lokacin da suka shiga damuwa.

Haka zalika malamin ya ce Bola Tinubu ya raba kudi ga gwamnoni da shinkafa ga ministoci domin su ba al’umma amma wasu sun ɓoye.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here