Gwamna Zulum ya Bayyana Cewa an Samo Mace 1 Daga Cikin ‘Yan Matan Chibok
Bayan shekara 7, an gano daya daga cikin yan matan Chibok.
An aurar da ita ga daya daga cikin yan ta’addan Boko Haram.
Sama da yan Boko Haram 100 sun mika wuya a makon nan kadai.
An ceto karin mutum daya cikin yan matan Chibok da aka sace a 2014, gwamnan jahar Borno Babagana Umara Zulum ya bayyana hakan ranar Asabar.
Yarinyar da aka ceto ta auri wani dan ta’addan Boko Haram ne kuma ta haifa masa yara biyu, gwamnan ya bayyana a gidan gwamnatin jahar dake Maiduguri.
A ranar 14 ga Afrilu, 2014, yan ta’addan Boko Haram sun yi awon gaba da dalibai mata kimanin 276 daga makarantar sakandaren mata dake Chibok, jahar Borno.
Karin yan Boko Haram 19 sun mika wuya ga jami’an Sojoji a Borno
Read Also:
An samu sabon nasara a yaki da yan ta’adda yayinda wasu yan Boko Haram/ISWAP suka mika wuya ga rundunar FOB dake Bama, jahar Borno.
A jawabin da Diraktan yada labarai na hukumar Soji, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ya saki ranar Laraba, 4 ga Agusta, yace mayaka 14 tare da iyalansu suka mika wuya.
Nwachukwu ya ce Sojojin sun karbi tubabbun yan ta’addan ne a cikin dajin Sambisa ranar Lahadi, 2 ga watan Agusta.
Bayan shekaru 7, ban fidda rai za’a ceto ‘yan matan Chibok ba: Gwamna Babagana Zulum
Gwamna Babagana Umara Zulum na jahar Borno ya ce da sannu za’a ceto dalibai matan da yan ta’addan Boko Haram suka sace a makarantar sakandaren Chibok a 2014.
Zulum ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki bayan shekaru bakwai da yan Boko Haram sukayi awon gaba da daliban yayinda suke shirin rubuta jarabawa.
Duk da cewa an ceto wasu daga cikin yaran, har yanzu akwai sauran daliban na hannun yan ta’addan.
A cewar Zulum, a matsayinsa na uba, ba zai iya jure ciwon rasa diya mace tsawon shekaru bakwai hannun yan ta’adda ba.