Kungiyoyin Malaman Jami’a SSANU da NASU Suna Zanga-Zangar Lumana a Abuja
Wasu kungiyoyin malaman jami’a sun fito zanga-zangar lumana a babban birnin tarayya Abuja.
Kungiyoyin sun fito ne dan nuna kokensu dangane da tsarin IPPIS.
Sun kuma bayyana kukansu na rashin biyan wasu daga cikin ma’aikatansu tsawon watanni shida.
Bangaren Jami’ar Bayero na Kwamitin Hadin Gwiwa na Manyan Ma’aikatan Kungiyar Jami’o’in Najeriya (SSANU) da kungiyar ma’aikatan jami’o’i marasa ilimi (NASU) sun shiga zanga-zanga alumana, Daily Trust ta ruwaito.
Sun shiga zanga-zangar ne a duk fadin kasar kan rashin kyakkyawan yanayin aiki watanni uku bayan Yarjejeniyar Fahimta da suka yi tare da gwamnatin tarayya.
Read Also:
Zanga-zangar wacce aka shirya za a kwashe kwanaki uku ana gudanar ta, ta jawo cece-kuce sakamakon jinkirin da gwamnatin tarayya ta yi na aiwatar da yarjejeniyar MoU tare da kungiyoyin kwadago a lokacin da suka fara yajin aikin gargadi na mako biyu don matsawa gida bukatarsu a Oktoba a bara.
Membobin kungiyoyin kwadagon sun hada baki sun bayyana korafinsu game da rashin tsari da ke tattare da sabon tsarin biyan albashi (IPPIS) wanda a karkashinsa aka ce wasu ma’aikatan sun yi asarar sama da 40% na albashinsu ba bisa ka’ida ba.
Wannan zanga-zangar na zuwa ne kusan mako guda da sake bude jami’o’in bayan rufe watanni tara saboda yajin aikin ASUU kan tsarin biya ta bai daya.
Zanga-zangar ta kasance ta hanyar jerin gwanon lumana daga filin taro na cibiyar zuwa ginin majalisar dattijai inda mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Adamu Sagir Abbas ya yi jawabi ga ma’aikata masu zanga-zangar.
Da suke gabatar da wasikar korafin ga VC don isar da su zuwa ga Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, Shugaban SSANU na Jami’ar, Dakta Haruna Aliyu ya gano rashin daidaito a cikin albashin su na wata saboda IPPIS a matsayin babban abin da ke damun su.
Sun kuma yi kira ga gwamnati da ta hanzarta aiki don magance matsalar kuma wataƙila wasu da ke cikin MoU ɗin da ta sanya hannu.