Kare Fararen Hula: Sudan ta yi Fatali da ƙudirin MDD
Sudan ta yi watsi da ƙudurin Majalisar Dinkin Duniya na girke jami’an tsaron ƙasashen duniya a ƙasar domin kare fararen hula.
Wata tawagar ƙwararru ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da rahoton gano mummunan halin tsananin cin zarafi da ta ce fararen hular ƙasar na fuskanta daga ɓangarorin da ke yaƙi da juna a ƙasar, a lokacin wani bincike da ta gudanar a wasu yankunan ƙasar.
Read Also:
Lamarin da ya sa ta bayar da shawarar samar da wata rundunar jami’an tsaron ƙasashen duniya da nufin kare fararen hula a ƙasar.
To sai dai ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta yi watsi da shawarar, inda ta kira ƙudurin da siyasa kuma haramtacce, sannan ta zargi ƙudurin da saɓa wa dokokinta.
Fiye da mutum miliyan 20 ne suka rasa muhallansu sakamako yaƙin da aka ɗauki fiye da shekara guda ana gwabzawa tsakanin sojojin gwamnati da dakarun RSF masu sanye da kayan sarki.
Yaƙin Sudan ya kasance ɗaya daga cikin manyan yaƙoƙin da suka ta’azzara ayyukkan jin-ƙai a duniya.