Sufeton ‘Yan Sanda Usman Alkali ya Bada Umarnin Dakatar da Abba Kyari
Sufeton ‘yan sanda IGP Usman Alkali ya ba da umarnin a gaggauta dakatar da Abba Kyari.
Wannan na zuwa ne yayin da korafe-korafe suka yi yawa kan zargin Abba Kyari da karbar rashawa.
A halin yanzu, an kafa wani kwamitin bincike kan Abba Kyari, wanda zai ba da rahoto nan kusa Abuja.
Sufeton ‘Yan Sandan IGP Usman Alkali Baba, ya nemi a ‘gaggauta’ dakatar da Abba Kyari daga aiki bisa zargin karbar cin hanci da ‘yan sandan Amurka ke yi masa kwanakin nan da ke da alaka da dan damfarar nan Abbas Roman Hushpuppi.
Read Also:
Baba, a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Frank Mba ya fitar, ya ba da shawarar dakatar da Kyari nan take inda aka fara bincike akansa, in ji rahoton Daily Trust.
IGP ya kafa wani kwamati na mutum hudu karkashin jagorancin DIG Joseph Egbunike domin bincikar zargin da ake yi wa Abba Kyari, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda kuma shugaban tawagar tattara bayanan sirri ta ‘yan sanda wato IRT.
Cibiyar bincike ta kasar Amurka (FIB) ta nemi hukumomin Najeriya su bincike Kyari bisa alakar cin hanci Hushpuppi da kuma taimaka masa ta wata hanya.
Meye alakar Hushpuppi da Abba Kyari?
Hushpuppi ya bayyana cewa ya bai wa Mista Kyari rashawar makudan kudade yayin da hukumar tsaron FBI ta Amurka ta kama shi bisa zargin aikata damfara da zamba a kan kamfanoni da daidaikun mutane a wasu kasashe.
Sai dai, rundunar ta ce har yanzu tana daukar Abba Kyari a matsayin maras laifi har sai bincike ya tabbatar da laifin nasa, in ji BBC Hausa.