Sule Lamido ya yi Martani Kan Tsige Shugaba Buhari
Alhaji Sule Lamido, tsohon gwamnan Jigawa ya ce bai dace a dinga kiraye-kirayen tsige Buhari ba.
Ya tabbatar da cewa wannan lamarin ba zai samu goyon bayan shi ba ko kadan.
Ya sanar da hakan ne a wani taron rantsar da shugabannin kananan hukumomi na Jigawa.
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya ce kiraye-kirayen da ake yi a kan tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari daga mulki bai dace ba kuma ba zai samu goyon bayansa ba.
Read Also:
Lamido, wanda ya sanar da hakan ga manema labarai yayin taron rantsar da shugabannin kananan hukumomi 27 da aka zaba a jiharsa, ya ce hakan kira ne kwatankwacin wanda ya dinga yi ga shugaban kasan.
Tsohon gwamnan wanda ya jaddada cewa bashi da wata matsala a tsakaninsa da shugaban kasa, ya kara da cewa yana kalubalansa ne saboda siyasa kuma da iya fadin gaskiyarsa.
Tsohon gwamnan, wanda ya yi magana a kan lamurran kasar nan daban-daban, ya tabbatar da cewa har yanzu lokacin cikar burinsa bai yi ba.
Ya kara da cewa abinda jam’iyyar PDP take bukata a halin yanzu shine daidaituwa da kuma hadin kai baki daya, jaridar Daily Trust ta wallafa.