Jerin Sunayen Matasan da Suke da Makudan Kudi a Najeriya
Hausawa su na cewa yaro da kudi, abokin tafiyar manya. Wannan rahoto na Legit.ng ya tattaro jerin matasan da suke da makudan kudi ne a Najeriya.
Kamar yadda za a gani, wadannan mutane masu matsakaitan shekarun sun yi arziki ne ta sanadiyyar watsa labarai, kimiyya da fasaha da harkar gidaje.
Watakila a cikin wadannan masu tasowa a samu wanda zai zama irin su Aliko Dangote nan gaba.
1. Igho Sanomi
Rahoton Newswirengr ya nuna Igho Snomi yana cikin attajiran matasa a Najeriya. Shugaban kamfanin na Cosmos oil AG da Taleveras ya ba $1bn baya.
Igho Sanomi ya yi kudi ne da harkar sadarwa, shigo da kaya ta jiragen ruwa da jiragen sama, sannan ya sa kudinsa a Taleveras wajen mai da kuma gas.
2. Ladi Delano
Idan ana maganar matasa masu kudi a kugunsu, akwai Ladi Delano wanda yana cikin wadanda suka kafa kamfanin na Moove wanda ake ji da shi a Afrika.
Read Also:
Delano ne ya kafa Solid XS wanda aka saya a 2008 a $15m. Daga nan suka cire $1bn, suka kafa kamfanin Bakrie Delano Africa, su na harkar sadarwa da fetur.
3. Obi Cubana
An fi sanin Obinna Iyiegbu da Obi Cubana a Najeriya, shi ne shugaban kamfanin Cubana Groups. A cikin taurari, ana tunanin babu mai kudinsa, Dala miliyan 500.
Obi Cubana ya yi kudi ne wajen saye da saida manyan kadarori, kwanan nan ya saye Odogwu Bitters.’Dan kasuwan mai shekara 47 ya shiga cikin wannan jerin.
4. Jowizaza
Joseph Eze Okafor wanda aka fi sani da Jowizaza, matashin mai kudi ne a kudancin Najeriya. Legit.ng Hausa ta ce Jowizaza ya ci gadon dukiyar mahaifinsa ne.
Ga wadanda ba su da labari, Joseph Eze Okafor shi shugaban kamfanin Jezco Oil Nigeria Ltd a yau. Dukiyar matashin sun fito ne wajen sha’anin gas da man fetur.
5. Seyi Tinubu
Seyi Tinubu ‘da ne ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, wanda kowa ya san shi a siyasar Najeriya. Ana tunanin matashin ya ba Dala miliyan 1.5 (N600m) baya a yau.
Rahotanni sun nuna Seyi Tinubu ne ya mallaki kamfanin Loatsad Promo media Ltd, wannan kamfani ya shahara, kuma ya yi kudi ne wajen yin tallace-tallace.