Sunayen Mutanen da Rundunar ‘Yan Sandan Jahar Ebonyi ta Take Nema
Rundunar ‘yan sanda a jahar Ebonyi sun bayyana sunan wasu mutane 18 da suke nema ruwa a jallo.
Yan sandan sun bayyana cewa suna zargin mutanen da hannu a tayar da tashe-tashen hankula tsakanin ƙabilu.
Jami’i mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jahar ne ya bayyana haka a wani saƙo da ya aike ma yan Jarida ranar Talata.
Rundunar ‘yan sanda reshen jahar Ebonyi sun bayyana wasu mutane 18 da suke nema ruwa a jallo da zargin rura wutar rikici tsakanin al’umma.
Read Also:
Wannan sanarwa na ɗauke ne a wani saƙo da jam’i mai magana da yawun yan sandan jihar, DSP Loveth Odah, ya aike ma yan jarida ranar Talata, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.
Sanarwar ta bayyana cewa ana neman mutanen ne sabida zargin su da aikata kisan kai, kunna wuta, ƙungiyar asiri da kuma ta’amali da makamai ba bisa ƙa’ida ba.
DSL Loveth Odah yace mutanen sune: “Sunayen mutanen sune Nwankwo Godwin wanda akafi sani da AKA, Hope Nwankwo, Chibueze Nwifuru wanda akafi sani babban nama, da kuma Daniel Nwangwoto.”
“Sauran sun haɗa da Osondu Mgbada (AKA taɓo), Okechukwu Nwanga (AKA Ezza), Chukwudi Nwite (AKA ɗan auta), Ernest Aduma, Chukwudi Okefi (AKA Mala’ika), Oliver Okefi (AKA Malife), Osondu Okefi da kuma Elom John,” inji shi.
“Paul Elom, Odinaka Idu, Monday Idu, Solomon Okefi, Chinedu Ilor da kuma Garba duk suna daga cikin waɗanda muke nema,” a cewarsa.