Jerin Sunayen ‘Yan Takarar Shugaban Kasa da APC ta Tantance
A yau ne jam’yyar APC ta fara atisayen tantance ‘yan takarar da za gwabza a zaben fidda gwaninta na makon nan.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da jam’iyyar ke daukar dumi kan wanda zai fito ya gaji Buhari a zaben 2023.
Ya zuwa yanzu, rahotanni sun ce akalla mutane tara ne suka tsallake tantancewar shugabannin jam’iyyar APC.
Abuja – Bayan kwashe makwanni ana shirye-shiryen gudanar da babban taronta zaben fidda gwani na shugaban kasa, ga dukkan alamu al’amura sun fara tafiya a jam’iyyar APC mai mulki inda a karshe ta fara tantance ‘yan takararta na shugaban kasa a yau Litinin.
Jam’iyyar wadda ta ci gaba da yin taron a cikakken sirri ta kuma hana ‘yan jarida zuwa wurin taron.
Shugaban kwamitin tantancewar kuma tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Cif John Odigie-Oyegun bai amsa tambayoyin da wakilin Vanguard ya yi masa ba game da taron.
Wannan ci gaban ya zo ne a daidai lokacin da jigo a jam’iyyar, Sanata Ali Modu Sheriff ya yi tir da wadanda suka kaddamar da yakin neman zabensa na shugaban kasa ta hanyar sanya hotunansa a wurare masu mahimmanci a fadin babban birnin kasar.
Read Also:
Ko da yake bai yi magana da ‘yan jarida ba, amma ta kara rura wutar rade-radin sauya shekarsa biyo bayan rashin nasarar da ya samu a zaben fidda gwani na gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Enugu.
Wadanda suka tsallake tantancewar shugabannin APC Bayanai da aka samo sun tabbatar da cewa 12 daga cikin 25 masu neman shugabancin kasar nan a APC sun tsallake atisayen tantancewa daga shugabannin jam’iyyar, inji rahoton Daily Sun.
Ga jerin wadanda aka tantance a yau Litinin:
1. Chukwuemeka Nwajiuba, tsohon karamin ministan ilimi
2. Abubakar Badaru, gwamnan Jigawa
3. Uji Kennedy Ohanenye (‘yar takara mace tilo)
4. Pastor Tunde Bakare
5. Sanata Robert Ajayi Borroffice
6. Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
7. Dave Umahi, gwamnan jihar Ebonyi
8. Sanata Ibikunle Amosun, tsohon gwamnan jihar Ogun
9. Felix Nicholas
10. Ken Nnamani
11. Rotimi Amaechi, tsohon ministan sufuri
12. Sani Yerima, tsohon gwamnan Zamfara
Wadanda za a tantance ranar Talata
Dimeji Bankole
Kayode Fayemi
Godswill Akpabio
Yemi Osinbajo
Rochas Okorocha
Yahaya Bello
Tein Jack-Rich
Christopher Onu
Ahmad Lawan
Ben Ayade
Ikeobasi Mokelu