Super Eagles ta Doke Cape Verde 2-1
Super Eagles ta je ta doke Cape Verde 2-1 a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ranar Talata.
Cape Verde ce ta fara cin Najeria ta hannun Dylan Tavares a minti na 20 da fara tamaula, minti 10 tsakani Super Eagles ta farke ta hannun Victor Osimhen.
Sauran minti 14 a tashi daga fafatawar Najeriya ta kara na biyu, bayan da Kenny Rocha Santos ya ci gida.
Da wannan sakamakon Super Eagles tana mataki na daya a rukuni na uku da maki shida, bayan buga wasa biyu.
Read Also:
Ranar Juma’a 3 ga watan Satumba Najeriya ta yi nasara a kan Liberiya da ci 2-0 a wasan farko na cikin rukuni a jahar Legas.
Jamhuriyar Afirka ta tsakiya ce ta biyu mai maki hudu, bayan da ta je ta ci Liberiya 1-0 ranar Litinin 6 ga watan Satumba.
Cape Verde ce ta uku a teburi na ukun da maki daya, sai kuma Liberiya ta hudu wadda ba ta da maki ko daya.
Super Eagles za ta karbi bakuncin Jamhuriyar Afirka ta tsakiya a wasa na uku a cikin rukuni ranar 9 ga watan Oktoba, a ranar kuma Liberiya ta karbi bakuncin Cape Verde.
Qatar ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya da za a yi a 2022.