AFCON 2025: Ba za mu Buga Wasa da Libya ba – Super Eagles

 

Kyaftin ɗin tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya – Super Eagles, William Troost-Ekong ya ce shi da ƴanwasan ƙasar sun yanke shawarar cewa ba za su buga wasa da Libya ba a wasan neman shiga gasar cin kofin Afirka ta 2025.

Troost-Ekong ya bayyana haka ne a shafinsa na X, inda ya bayyana rashin jin daɗinsa game da halin da suka tsinci kansu bayan isar su Libya domin buga wasa a ranar Talata.

Ƴanwasa da jami’an tawagar ƙwallon ƙafar Najeriya ta Super Eagles sun tsinci kansu cikin wani yanayi bayan da suka shafe kusan awa 15 a filin jirgin sama na Abraq da ke Libya.

A yammacin ranar Lahadi ne, tawagar Super Eagles ta isa Libya domin buga zagaye na biyu na wasan neman shiga gasar kofin ƙasashen Afirka ta 2025 da za a yi a Morocco.

Hakan na zuwa ne bayan da hukumomin Libya suka tilasta jirgin Super Eagles sauka a filin jirgin sama na Abraq, maimakon filin jirgin saman Benghazi da tun asali aka tsara ƴanwasan za su sauka, kamar yadda hukumar kwallon ƙafa ta Najeriya NFF ta bayyana.

Najeriya da Libya za su ɓarje gumi ne a zagaye na biyu na wasan a ranar Talata.

A wasan farko da aka buga a Najeriya, Super Eagles ɗin ce ta doke Libya da ci ɗaya da nema.

Hotuna da bidiyo da NFF ta fitar a shafukan sada zumunta sun nuna yadda yanwasan na Super Eagles suke zaune dirshan a filin jirgin saman, inda suke ta hira bayan shafe fiye da sa’o’i 12 cikin jirgi daga Najeriya zuwa Libya.

Hukumomi sun ce bayan nan, ƴanwasan kuma za su sake saɓar titi inda za su yi tafiyar awa uku a mota daga Abraq zuwa Benghazi wurin da za su taka leda.

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Libya ma ta yi ƙorafi kan yadda hukumomin Najeriya suka ajiye su tsawon sa’o’i lokacin da jirginsu ya sauka a ƙasar a wasan farko da suka je yi.

Wani abu da ke ci gaba da ɗaure wa mutane kai a shafukan sada zumunta shi ne ko abin da ya faru ramuwar gayya ce da hukumomin Libya suka ɗauka kan abin da suka ce ya faru da su a Najeriya.

Kyaftin ɗin na Eagles ya ce akwai buƙatar hukumar ƙwallon kafa ta Afirka CAF ta yi duba kan yanayin da suke ciki da kuma abin da ke faruwa da su a Libya.

A cewarsa “ba za mu yarda mu je ko ina ta titi ba, ko da kuwa da tsaro, babu mu da tabbacin tsaro. Idan muka amince da haka, kuna iya tunanin yanayin da masaukinmu ko abincin da za su ba mu zai kasance.”

 

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here