Super Eagles za ta Buga Wasan Sada Zumunta da Saudi Arabia
Tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, Super Eagles za ta buga wasan sada zumunta da Saudi Arabia ranar Juma’a 13 ga watan Oktoba a Portugal.
Super Eagles za ta buga karawar ce, bayan wata daya tsakani da ta ci Sao Tome 6-0 a wasan karshe a rukunin farko ta kuma samu gurbin shiga gasar kofin Afirka da za a yi a 2024 a Ivory Coast.
Nigeria za ta buga karawar ce domin gwada ‘yan wasan da za ta fuskanci Lesotho a karawar neman gurbin shiga gasar kofin duniya da za a yi a 2026.
Read Also:
Super Eagles za ta kuma fuskanci Zimbabwe a wasa na biyu a neman shiga babbar gasar tamaula ta duniya da za su kece raini a cikin watan Nuwamba.
Tawagar Saudi Arabia da ake kira Green Falcons za ta fara fafatawa da ta Mali, kwana hudu tsakani ta fuskanci Super Eagles.
Ita kuma Najeriya kafin ta kara da Saudi Arabia kwana uku tsakani, za ta fuskanci Mozambique a dai wasan na sada zumunta.
Wannan shi ne karon farko da Najeriya da Saudiyya za su kece raini tsakanin manyan tawaga, amma Nigeria ta yi nasara a kan Saudi Arabia a 1989 a Fifa U20.
An buga karawar a Riyadh, inda Chrstopher Ohenhen da kuma Mutiu Adepoju suka ci wa Najeriya kwallayen.
Filin wasa na Estadio Municipal de Portimão da ke Algarve a Portugal da zai karbi bakuncin wasa na kungiyar Portimonense S.C. mai cin ‘yan kallo 10,000.