Dalilin Tabarbarewar Ilimi a Najeriya – Sarkin Anka
Shugaban majalisar sarakunan Zamfara kuma sarkin Anka, ya alakanta tabarbarewar ilimi da auren mace fiye da daya.
Alhaji Attahiru Muhammad Ahmed ya ja kunnen maza a kan auren mace fiye da daya saboda hakan ke hana a samu ilimi mai nagarta.
Read Also:
Ya bayyana hakan ne a taronsa da sarakuna 17 na jahar Zamfara tare da shugaban hukumar UBE ta jahar baki daya Shugaban majalisar sarakunan jahar Zamfara kuma Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Muhammad Ahmed ya ja kunne a kan auren mace fiye da daya wanda yayi ikirarin shine dalilin tabarbarewar ilimi a kasar nan.
A yayin magana a taron sarakunan jahar 17 da shugaban UBE na jahar Zamfara, Alhaji Abubakar Aliyu Maradun a Gusau, Sarkin Anka wanda ya fara alakanta talauci da tara mata, yayi kira ga al’ummar Musulmi da su tabbatar da sun bai wa ‘ya’yansu ilimi na boko da zamani mai nagarta.
Basaraken ya jaddada goyon bayan sarakunan gargajiya ga ilimin zamani a jahar Zamfara da jama’arta baki daya, Linda Ikeji ta wallafa.