Sai na tabbatar da Adalci ga iyalan Wanda Dogarina ya Harbe – Gbajabiamila

 

Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai ya bayyana sunan jami’in tsaron da ya bindige wani magidanci a Abuja.

Gbajabiamila ya yi alkawarin ganin an tabbatar da adalci kan lamarin.

Ya bayyana alhininsa ga iyalan mamacin kuma yayi alkawarin taimaka musu.

Kakakin majaisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila, ya bayyana sunan dogarinsa da ya bindige wani mai sayar da jarida a Abuja, Ifeanyi Okereke, ranar Alhamis ba gaira ba dalili.

Gabjabiamila ya ce sunan jami’in tsaron Abdullahi Hassan, kuma tuni ya mika shi hannun hukumar DSS domin hukunta shi.

A jawabin da ya saki ranar Juma’a, Kaakin ya ce ya cire jami’in daga cikin masu tsaronsa yanzu.

“Da safen nan na mika jami’in tsaro, Abdullahi M. Hassan, hannun hukumar DSS domin bincike da hukuncin da ya dace,” yace.

“A yanzu dai na dakatad da shi daga tawagar dogarai na.”

Kakakin ya jaddada cewa babu wani dalilin da zai sa a hallaka rayuwan mutum haka kawai.

“Mutuwar Mr Ifeanyi Okereke a hannun daya daga cikin jami’an tsaro na ya matukar girgiza ni.

Mr Okereke dan kasa ne wanda ke neman abincinsa da na iyalansa,” yace “Sai na tabbatar da cewa iyalan Okereke sun samu adalci.”

“Na aika sakon ta’aziyya na ga iyalansa kuma na shirya haduwa da iyayensa.” “Bayan haka, na yi alkawarin taimakawa matarsa da yaran da ya bari.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here