Ina Fatan Za’a Tabbatar da Kare Ruyuwar ko Wanne ‘Dan kasa – Paparoma ga Gwamnatin Najeriya

 

Paparoma Francis ya yi kira ga gwamnatin Najeriya ta tabbatar da kare rayukan al’ummar kasar biyo baya ga mugayen hare-haren da ke faruwa a arewacin kasar.

Paparoman ya yi addu’a ga wadanda su ka rasa rayukansu da kuma wadanda su ka ji rauni sakamakon rashi tsaro, ganin harin da aka kai jahar Kaduna a karshen makon da ya gabata wanda ya jawo mutuwar gomman mutane.

Ranar Laraba a wani zama da ya ke yi da magoya bayan sa duk sati a fadar Vatican,ya bayyana rashin jin dadin sa game da harin da aka kai ranar Lahadin da ta gabata a kauyukan Madamai da Abun da ke arewacin Nigeria.

Ya kara da cewa,‘’ina fatan za’a tabbatar da kare rayuwar ko wanne dan kasa.”

Yankin arewacin Najeriya na fama da rashin tsaro na tsawon shekaru, wanda ya hada da hare-haren yan fashin daji da na masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here