ISWAP: Gwamnatin Najeriya ta Tabbatar da Mutuwar shugaban Kungiyar, Al-Barnawi
Rundunar sojan Najeriya ta tabbatar da mutuwar Abu Musab al-Barnawi, wanda shi ne shugban ƙungiyar IS na Yammacin Afirka wadda aka fi sani da ISWAP.
“Ya mutu kuma zai ci gaba da kasancewa matacce,” a cewar Hafsan Hafsoshin Tsaro Janar Lucky Irabor.
Sai dai Janar Irabor bai bayar da wani ƙarin bayani ba game da mutuwar Barnawi, wadda aka fara ruwaitowa a watan Satumba.
Ƙungiyar ta ISWAP ba ta ce komai ba game da lamarin, wadda ake yi wa kallon ƙungiyar masu iƙirarin jihadi mafi ƙarfi a Najeriya tun bayan mutuwar shugaban Boko Haram Abubakar Shekau a farkon wannan shekarar.
Bayan haka ne kuma mayaƙan Boko Haram ɗin suka dinga miƙa wuya ga ISWAP da kuma sojojin Najeriya.