Lokaci ya yi da za a Tabbatar da Sahihi Kuma Ingantaccen Zaɓe a Najeriya – Injiniya Yusuf Yabagi

Masu ruwa da tsaki a lamuran zabe a Najeriya sun fara tsokaci kan sa hannun da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kan kudurin dokar zabe ta 2021 da aka dade ana ce-ce-ku-ce a kai.

Buhari ya saka hannu kan dokar ne a yayin wani takaitaccen buki a fadarsa a gaban idon shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai da kuma shugaban hukumar zaben kasar da sauransu.

Shugaban majalisar tuntubar juna tsakanin jam’iyyun siyasar kasar wato Inter Party Advisory Council (IPAC), Injiniya Yusuf Yabagi San, na daga cikin wadanda suka shaidi sa hannun, kuma ya shaida wa BBC cewa wannan lokaci ne mai cike da tarihi.

Injiniya Yabagi ya ce lokaci ya yi da za a tabbatar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe a Najeriya.

”Zaɓe a Najeriya zai zamo abin da mutane za su amince da ingancinsa, za a kaucewa matsalolin da aka fuskanta a baya, da rage kashe kudi marasa ma’ana, don haka sanya hannu kan wannan doka ba karamin abu shugaba Buhari ya yi wa tarihin Najeriya ba.

Saboda yawancin matsalolin da ake fama da su a kasar nan su na samo asali tun daga rashin shugabanci na gari, da zarar babu hanyar da za a fito da shugabanni na gari ta hanyar zabe, za a ci gaba da tafiya mai kunci da rashin tabbas.”

Yabagi ya kara da cewa wannan doka za ta magance matsalar satar kuri’u, ko akwatin zaben baki daya da matsalar da ake samu wajen kidaya kuri’u ta hanyar murdiya da ake yi a baya.

A cewarsa wannan zai kawo sauki saboda zabe ya na nan cikin na’ura ba kamar a baya da sai kowanne baturen zabe na mazaba ya kai sakamako inda ake tattara shi ba.

Sai dai kuma Injiniya Yabagi ya ce a fanin kazamin kudi da ake amfani da shi a lokacin zabe, wannan doka babu abin da za ta iya yi akai.

Yana mai cewa Jami’an tsaro ne kadai suke da hurumi anan domin abi hanyoyin da za a rage aikata hakan,” in ji Yabagi.

Kafin rattaba hannu kan dokar zaɓen sai da shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci ‘yan majalisa su sake komawa domin yin gyara a sashe na 84, wanda ya ce an haramtawa masu rike da mukaman gwamnati yin zaɓe a tarukan jam’iyya ko zaɓen ‘yan takara.

Yabagi ya ce su na goyon bayan wannan matakin ganin ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya, bai kuma kamata a ce an hana wani ɗan kasa damar da ya ke da ita ba.

A ranar Juma’a ne, Shugaba Muhammadu Buhari ya saka wa sabuwar dokar hannu bayan da aka dauki tsawon lokaci ana kace-nace a kai.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here