Hotuna: Tagwaye Maza Sun Auri Tagwaye Mata a Kano

Yawanci akan ga tagwaye masu kama da juna na abubuwa iri daya kamar sanya tufafi kala daya, yawo a tare, karantar abu daya a makaranta ko ma yin aure rana daya.

Abin da ba a saba gani ba shi ne su auri tagwaye ‘yan gida daya masu kama da juna kuma a lokaci guda.

To sai dai Hassan Suleiman Indabawa da Hussein Suleiman Indabawa, tagwaye masu kama da juna, mazauna unguwar Dan-Agundi ta Karamar Hukumar Birnin Kano da Kewaye sun kafa tarihiarihi inda suka angwance da wasu tagwayen ‘yan gida daya masu kama da juna, Hassana Ado Ashir da Husseina Ado Ashir na Unguwar Dabai a Karamar Hukumar Gwale, Jihar Kano a ranar Lahadi 22 ga watan Nuwamba, 2020.

Ba wai kawai auren juna suka amince su yi ba, hatta zamansu ma sun amince a gida daya za su zauna domin ci gaba da yaukaka dankon zumunci.

Da ma dai ko a addinance da a al’adance, tagwayen na da damar su auro ‘yan uwan juna a matsayin matayensu.

A tattaunawarsa da Aminiya, daya daga cikin angwayen, Hassan Suleiman ya ce babban makasudinsu na auro tagwayen shi ne saboda su tsawaita dankon zumuncinsu har zuwa ga matansu ta yadda su ma za su rika kallon kansu a matsayin daya.

Angwaye da amaren

A cewar Hassan, “Tun da aka haife mu komai tare muke yi ba wani bambanci, duk abin da kowa ya mallaka na kowa ne.

“A kan haka ne muke ta addu’a a kan Allah Ya sa matansu su ma su kasance suna da ra’ayi da tsari irin namu.

“Ko da Allah Ya yi wa daya daga cikinmu arziki, idan yana tallafa wa dan uwansa, matarsa ba za ta ji kyashin yana yin haka ba, saboda ‘yar uwarta ake yi wa.

“Ka ga yanzu ko da ‘ya’yanmu muka yi wa ba wacce za yi kishi, tunda su ma iyayensu daya kamar yadda muke,” inji Hassan Indabawa.

Hassan da Hussein dai dukkansu sun yi karatun Difloma a Kwalejin Fasaha ta Kano, da kuma wata Diflomar daban a Kwalejin Koyon Tsafta ita ma ta Kanon kuma yanzu haka suna aiki a Sashen Kula Da Lafiya a Matakin Farko na Karamar Hukumar Gwale.

Sun ce babban burinsu yanzu a rayuwa shi ne su ma Allah Ya albarkace su da tagwaye a matsayin zuri’a.

“Dukkan yayyenmu maza guda biyar sun haifi tagwaye, addu’armu ita ce mu ma Allah Ya sa mu samu”, inji Hussein Indabawa.

Abin sha’awar da ban al’ajabi shi ne Hassan ne ya auri Hassana, yayin da kuma Hussein ya auri Hussaina.

Yadda suka fara haduwa

Hassan ya ce kwatancensu aka yi musu cewa ‘yan matan suna da ra’ayi irin nasu kuma za su dace da juna.

A nasu bangaren kuwa, amaren (Hassana da Husseina) wadanda yanzu haka suke karantar Ilimin Sinadarai a Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Kano sun ce mu’amalarsu ta fara ne da abota kafin daga bisani ta rikide zuwa soyayya, har ga shi an kai ga daura aure.

Hassana ta ce, “Gaskiya abin da kawai zan ce shi ne wannan aure hadin Allah ne. Da farko dai a matsayin abokanmu suke, kasancewarmu tagwaye ‘yan uwanmu, ban ma san lokacin da kawancen ya juye ya koma soyayya ba.

“Mukan je mu ziyarci iyayensu a gida, su ma kuma sukan zo gidanmu, dangantakarmu ta yi karfi sosai tun ma kafin mu fara soyayya.

“Ko hira suka zo wurinmu a matsayin samari da ‘yan mata mu hudun muke zama mu yi hira. Ba ma warewa ko kowace ta kebe da saurayinta, saboda muna kallon junanmu a matsayin daya”, inji Hassana.

Ita kuwa Husseina cewa ta yi tun kuruciyarsu ake musu addu’ar su auri tagwaye kamarsu saboda zumuncinsu ya dore, tana mai cewa auren nasu yanzu alama ce ta amsa addu’ar da aka jima ana yi musu.

“Tagwaye da dama sun zo wajenmu, amma ba mu taba soyayya da kowa ba in ba wadannan ba.

“Akwai ranar ma da ba zan manta ba mun taba zuwa kasuwa sayayya sai mai sayar da kayan yake ce mana gaskiya akwai wasu tagwaye kamarku, ina ma a ce su zaku aura. Lokacin bai ma san tuni an yi baikonmu da su ba.

“Da na fada masa da su aka yi mana baikon kar ka ga yadda ya taya mu murna yana kuma cike da mamaki,” inji Husseina.

Hassana da Husseina sun kuma ce babban burinsu a rayuwa shi ne su zama likitoci a nan gaba in suka kammala karatunsu.

Ita ma a zantawarta da Aminiya, kanwa ga angwayen wato Gambo (Fadila Suleiman) ta ce duk da irin farin cikin da take cike da shi cewar yayyenta za su auri tagwaye, za ta yi kewarsu matuka.

“Ko da yake ni mace ce, mun kasance muna yin abubuwa tare da su a mafi yawancin lokuta. A zahirin gaskiya ma, ji nake kamar ni da su ‘yan uku ne ba tagwaye ba”, inji Gambo.

An daura auren ne a Masallacin Juma’a na Karmawy dake dab da Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano, a misalin karfe 11:00 na safiyar Lahadi, 22 ga watan Nuwamban 2020.

Daga: Aminiyya DailyTrust

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here