Hujjar da yasa na Saka wa Tagwayena Sunan Buhari da Al-Makure – Gwamnan Nasarawa

Gwamnan jihar Nasarawa ya rada wa tagwayensa sunan shugaba Muhammadu Buhari da na Umar Al-Makura.

Ya ce ya rada wa yaransa sunayensu ne saboda darajawa da mutuntawa da ke tsakaninsa da shugabannin biyu.

Manyan masu fadi a ji, kamar mataimakin gwamnan jihar, kakakin majalisar jihar da sauransu sun halarci taron.

Gwamnan jihar Nasarawa ya rada wa tagwayensa sunan Shugaba Muhammadu Buhari da na Sanata Umar Tanko Al-Makura, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Bayan amaryar gwamnan, Hajiya Farida Abdullahi Sule, ta haifi zankada-zankadan tagwayenta, an yi shagalin sunan a ranar Talata a cikin fadar sarkin Gudu a karamar hukumar Akwanga, Alhaji Sule Bawa, wanda shine mahaifin gwamnan.

Gwamnan ya ce: “Na radawa yarana sunayen shugaba Muhammadu Buhari da na Sanata Umar Tanko Al-Makura saboda girmamawa ta a garesu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here