Najeriya Tana da Tarin Arziki – Osinbajo
Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce Najeriya tana da arziki.
Ya ce kasar nan ta tara duk wani abu da kowacce kasa take nema don ta daukaka.
Ya fadi hakan a ranar Talata a wani taro na NASIDRC da aka yi a Lafia, jihar Nasarawa.
Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce Najeriya tanada duk wasu abubuwan da ya kamata ta samu don ta daukaka.
Read Also:
Ya fadi hakan a ranar Talata, lokacin da ya je wata kaddamarwa ta NASIDRC a Lafia, jihar Nasarawa, jaridar Daily Trust ta wallafa.
Inda yace Najeriya tana da duk wani abu da kasa take bukata, tana da masu fasaha, maza da mata, masu tunani da ma’adanai iri-iri wadanda ake nema don kasa ta daukaka.
“Gwamna Abdullahi Sule ya nuna halayen shugabanci nagari saboda cigaba da ayyukan da gwamnatin da ta gabacesa ta fara, Gwamna Umaru Tanko Al-Makura, na asibitin kwararru na Dalhatu Araf (DASH), Lafia.
“Jihar Nasarawa ba ta fi kowacce jiha arziki ba a Najeriya. Kuma idan aka dubi kudaden da Nasarawa take samu, da kuma wadanda ake bata, bata daya cikin jihohi 3 na sama,” yace.