An Samu Takaddama a Majalisar Dattawan Najeriya Kan Nada Sabbin Shugabannin Marasa Rinjaye

 

An samu takaddama a majalisar dattijan Najeriya ranar Talata, bayan sanar da nadin shugabanni a bangaren marasa rinjaye da Shugaba Majalisar Godswill Akpabio ya yi.

Kujerar shugaban marasa rinjaye da ta mai tsawatarwa a bangaren marasa rinjaye sun kasance babu kowa tun bayan da kotun daukaka kara ta soke zaben Sanata Simon Davou Mwadkwon na PDP da Darlington Nwokocha na LP.

Kotu ta soke zaben sanata Simon Mwadkwon inda ta ba da umarnin sake gudanar da zabe.

Tun a makon jiya ne sanatocin jam’iyyar PDP suka gudanar da wani taron gaggawa kan batun maye guraben shugabannin marasa rinjaye.

Jaridar Punch ta ambato Sanata Garba Maidoki wanda ya yi jawabi ga manema labarai bayan taron, na cewa ‘yan majalisa bangaren adawa sun amince sun amince da fitar da sabon shugaban marasa rinjaye daga arewa ta tsakiya.

Don haka, yayin zaman majalisar na Talata, Godswill Akpabio ya sanar da Abba Moro na PDP a matsayin shugaban marasa rinjaye, yayin da Osita Ngwu shi ma daga PDP zai kasance mai tsawatarwa a bangaren marasa rinjaye.

Shugaban majalisar ya ce sabbin shugabannin marasa rinjayen sun samu rinjayen goyon bayan takwarorinsu.

Da yake gabatar da wnai kudurin jan hankali, Sanata Okechukwu Ezea na jam’iyyar LP ya nuna rashin amincewa da rashin shigar da jam’iyyarsa a shugabancin marasa rinjaye, inda ya bayyana lamarin a matsayin rashin adalci ga jam’iyyun marasa rinjaye.

Ana cikin hargitsi ne, sai Sanata Tony Nwoyi na LP ya zargi Godswill Akpabio da nada wa jam’iyyun adawa shugabanci.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com