An bayyana Malam Salihu Sagir Takai na jam’iyyar PRP a matsayin wanda yafi dacewa da ya zama Gwamnan jihar Kano na gaba. Mai sharhi kan al’amuran kasuwanci Alhaji Ali Sabo Yakasai ne ya bayyana hakan a wata mukala da ya aiko mana.

“Yanzu mun fahimci komai ingancin Shugaba, kuma komai nagartarsa idan bai samu wadanda zasu tallafa masa gudanar da mulki ba to akwai matsala, saboda yana tubkane baya na warwarewa. Yanzu kalli Shugabanmu, Babanmu abun alfaharinmu Muhammad Buhari irin kokarin da yake wajen inganta rayuwar talaka. Bawan Allan nan Muhammadu Buhari har rashin lafiya ta kusa halakashi amma dattijon nan ya tsaya tsayin daka dan ceto rayuwar talaka.

Amma a gefe guda munyi rashin saa na Gwamnoni a arewa yawancinsu ba talakawa ne a gabansu ba, babu kishi, da ka suke tafiya, babu manufa ta inganta rayuwar talaka. Don haka wajibi ne mu sake tunani wajen samar da Gwamnoni masu inganci wadanda suke da akida da tsayuwa irinta Baba Buhari, kuma ko baa jamiyyar APC suka fito ba su yakamata mu goyawa baya domin su mulke mu.

Jihar Kano tana fama da irin wannan matsalar. Kano ne garin da yafi baiwa Baba PMB yawan kuriu. Amma ayyukan jihar Kano sabanin ayyukan Gwamnatin Baba Buhari ne. Harkar noma, noman rani da kiwo tun zamanin tsohon Gwamna Audu Bako (Allah ya kai rahama cikin kabarinsa) an barshi. Sai kuma Gwamna Abubakar Rimi da ya bude KASCO da KNARDA domin inganta noma.

Hanyar kasuwanci da masanantu da hanyoyin da zaa bunkasasu ko kusa baa dauki hanyar su ba, Kuma anyi halin ko in kula dasu. Kuma a gefe guda shine manufofin Gwamnatin Baba Buhari don inganta noma, kasuwanci da masanaantu

Zabinmu ga Salihu Sagir Takai na jamiyyar PRP zai dace da tafiyar Baba Buhari ta wajen rikon amana da jajircewa da karban shawarwarin kwararru da kuma kafewa domin aiwatar da su.

Salihu Takai tested and trusted ne, yana kama da Baba Buhari sosai ta wajen manufa iri daya. Salihu Takai yayi Chairman na Takai local Government ya kuma rike Chairman da inganci da bin sharia ta adalci. Duk dan local Government na Takai zai fadi alherinsa na rashin son kai da babakere.

Salihu Takai shi ya rike commissioner na gidan ruwa inda yayi katafaren gidan ruwa mafi girma a Africa ta yamma a wanda bayan kammala aikin ne ya dawo da rarar kudi Naira Miliyan 500 da suka yi ragowa.

SalihuTakai shine ya rike commissioner na local Government bisa Amana ta wajen baiwa dukkan local Government 44 hakkokinsu ba tare da ya dauki ko kuma a bashi ko sisin kwabo ba. Wannan abu sananne ne.

Salihu Takai kamar Buhari yake, yayi takara har sau 3 amma Allah bai bashi dama ba. Gashi yanzu Allah ya kaddara fitowa ta hudu a karkashin jamiyyar PRP. Jamiyyar Mallam Aminu Kano. Jagoran talakawa.

Buhari da Aminu Kano suna yaki akan danne talaka da yakar yan tamore masu zukar jinanai ba marasa galihu da raunana. Salihu Takai takalminsa yayi daidai da irin wadannan gwarazan mutane bayin Allah. Muna fata Allah ya bashi wannan kujera ta jihar Kano kuma ya kasance tare dashi. Ya fishsheshi zamewa. Amin”

The post Takai ne yafi dacewa da Kano a wannan lokaci – Ali Yakasai appeared first on Daily Nigerian Hausa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here