Tankar Gas ta yi Sanadiyya Mutuwar Mutane da Dama a Abuja

 

FCT Abuja – Rahotanni sun nuna cewa wata tankar gas ta tarwatse a gadar Karu da ke kan titin Abuja-Nyanya-Keffi a babban birnin tarayya Abuja jiya Laraba 19 ga watan Maris.

Lamarin ya faru ne da yammacin Laraba, inda motoci da dama suka ƙone, wanda ya sa aka fara fargabar yuwuwar asarar rayuka da dama.

Wata shaidar gani da ido, Fatima Diamond, ta shaida wa jaridar Daily Trust a wata tattaunawa ta wayar salula cewa iftila’in ya faru ne cikin ƙanƙanin lokaci kuma a tsakiyar jama’a.

Yadda fashewar tankar ta faru a Abuja

Haka nan, gobarar da ta tashi sakamakon hatsarin babbar mota ta haddasa cunkoso mai tsanani a wannan yanki da ke da yawan zirga-zirgar ababen hawa a Abuja

Fatima Diamond ta ce:

“Abin ya faru cikin ƙankanin lokaci. Motoci da dama sun kone, ni da kaina na kidaya motoci biyar da gobarar ta shafa.

“Amma na ji ana cewa sama da motoci 20 ne suka lalace. Sai da na yi amfani da babur domin tserewa daga wurin.”

Masani kuma mai sharhi kan harkokin yaƙi da ta’addanci, Zagazola Makama ya tabbatar da aukuwar lamarin a shafinsa na X.

Mutane sun shiga firgici da wuta ta kama

Zagazola Makama, ya ruwaito wasu shaidu suna bayyana yadda mutane suka shiga firgici suna gudu domin tsira da rayukansu.

Ya ce mummunan hatsarin ya afku ne yayin da babbar motar dakon kaya mai ɗauke da iskar gas ta samu tangarɗar birki, ta kwacewa direba sannan ta yi kan motoci.

An ruwaito cewa motocin da ke kusa da wurin sun kama da wuta nan take, kuma galibinsu suna ɗauke da fasinjoji.

Rahotanni na farko sun nuna cewa babbar motar tana dauke da kwantena cike da iskar gas (CNG) tare da man fetur.

Jami’an agaji, ciki har da ma’aikatan kashe gobara da likitoci, sun garzaya wurin don kokarin shawo kan gobarar tare da taimakon wadanda abin ya shafa.

Ana fargabar mutane da dama sun mutu

Wani wanda ya tsira daga gobarar ya bayyana cewa:

“Na ga motar tana tahowa da gudun tsiya, tana kokarin karkacewa kafin ta bugi wasu motoci. Cikin dan lokaci, sai kuma ta fashe, wuta kuma ta kama ko ina.”

Har yanzu ba a tantance yawan wadanda suka rasa rayukansu ba, amma jami’ai na fargabar cewa adadin mutanen da suka mutu ya yi yawa, la’akari da yadda gobarar ta yi tsanani.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here