Jawabin Mataimakin shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo a Kan Tsayawa Takarar Shugaban ƙasa a 2023

 

Mataimakin shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana matsayarsa a kan takarar shugabancin ƙasar nan bayan kammala wa’adin Buhari.

Mr. Osinbajo yayi watsi da wani shafin yanar gizo da wasu mutane ke ɗaukar nauyi, wanda ke bayyana cewa mataimakin shugaban zai nemi takara a 2023.

Mataimakin shugaban ya bayyana cewa har yanzun bashi da sha’awar tsayawa takara, ya maida hankali ne kan aikin ofishin sa na yanzu.

Ofishin mataimakin shugaban ƙasa yace gasar neman tikitin takarar shugabancin ƙasar nan a zaɓen 2023 yana daɗa jan hankali, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Sai dai ofishin ya bayyana cewa mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, bashi da niyyar yin takarar shugaban ƙasa a yanzu. Kakakin mataimakin shugaban, Laolu Akande, shine ya faɗi haka a wani jawabi daya fitar yau a babban birnin tarayya Abuja.

Yace Mr. Osinbajo bashi da alaƙa da waɗanda ke yaƙin neman zaɓensa a yanar gizo.

Akande yace:

“An jawo hankalin ofishin mataimakin shugaban ƙasa kan wani shafin yanar gizo mai suna supportosinbajo.ng, wanda yake kira ga yan Najeriya su shigo tawagar yan sa kai domin nuna goyon bayansu ga Osinbajo yayin da zaɓen 2023 ke gabatowa.”

“Bayanan wannan shafin yanar gizon da neman agajin da suke yi yana cigaba da jan hankalin masu amfani da dandalin sada zumunta na whatsapp, kuma suna faɗin cewa Osinbajo ya amince zai yi takara amma a ɓoye.”

“Ofishin mataimakin shugaban ƙasa bashi da wata alaƙa da wannan shafin yanar gizo ko tawagar mutanen dake ɗaukar nauyin shi, Osinbajo bai nuna sha’awar tsayawa takarar kowace kujera ba a zaɓen 2023.”

“Amma ya maida hankali wajen aikinsa na mataimakin shugaba a wannan gwamnatin wajen ƙoƙarin shawo kan duk wani abu daya taso a ƙasa, da kuma kulawa ga yan Najeriya.” Inji shi. Mr. Osinbajo shine abokin takarar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a zaɓen shugaban ƙasa na 2015 da 2019.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here