Matsalar Tsaro: Gwamnonin PDP 13 Sun Shiga Ganawa

 

Wasu gwamnoni a karkashin inuwar jam’iyyar PDP sun shiga tattaunawar sirri kan batun tsaro.

Gwamnonin 13 suna ganawa ne a jahar Oyo, inda ake sa ran isowar wasu sauran gwamnonin.

Ana sa ran za su tattauna kan batun rashin tsaron Najeriya da kuma ci gaban jam’iyyarsu ta PDP.

Gwamnonin jahohi 13 a karkashin jam’iyyar PDP, a yanzu haka suna ganawa a Cibiyar Taron Kasa da Kasa na Cibiyar Kula da Noma ta IITA dake Ibadan ranar Litinin, Daily Nigerian ta ruwaito.

Gwamnonin su ne:

Aminu Tambuwal na jahar Sakkwato; Samuel Ortom na Benue; Douye Diri na Bayelsa; Okezie Ikpeazu na Abia da Emmanuel Udom na Akwa Ibom.

Sauran sune:

Ifeanyi Okowa na Delta, Ifeanyi Ugwuanyi na jahar Enugu, Umar Fintiri na Adamawa; Bala Mohammed na jahar Bauchi, Nyesom Wike na Ribas da Godwin Obaseki na Edo. Akwai kuma gwamna mai masaukin baki, Seyi Makinde na Jahar Oyo da Mataimakin Gwamnan Zamfara, Aliyu Gusau wanda ya wakilci Gwamna Bello Matawalle.

Ana sa ran Gwamna Darius Ishaku, na Taraba da Gwamna Ben Ayade, na Kuros Riba za su shigo yayin da taron ke ci gaba. Gwamnonin da suka iso cibiyar taron daidai karfe 1:10 na rana a cikin motar bas sun shiga ganawar sirri.

NAN ta tattaro daga wurin taron cewa taron zai mayar da hankali ne kan yanayin tsaro a kasar.

Ta kuma tattaro cewa taron wanda Shugaban gamayyar gwamnonin PDP ya jagoranta, Gwamna Aminu Tambuwal zai tattauna wasu batutuwan da suka shafi ci gaban jam’iyyar.

Ana sa ran za a fitar da sanarwa bayan taro.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here