Jerin Takunkumai 10 da Birtaniya ta Saka wa Rasha

Waɗannan su ne jerin takunkuman da Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya sanar da saka su a kan Rasha:

1.Za a riƙe dukkan ƙadarorin bankunan Rasha kuma za a cire ta daga tsarin harkokin kuɗin birtaniya. Wannan zai hana su samun damar amfani da kuma cire kuɗaɗe ta Birtaniya.Hakan ya haɗa da rufe bankin VTB ba tare da ɓata lokaci ba

2.Majalisar Dokoki za ta dakatar da manyan kamfanonin Rasha da kuma ƙsar daga aron kuɗaɗe a kan kasuwannin Birtaniya

3.Za a riƙe ƙadarorin mutum 100

4.Za a haramta wa jiragen kamfanin Aeroflot sauka a Birtaniya

5.Za a dakatar da lasisan ba da damar a yi abubuwan da suka shafi harkokin soji

6.A cikin kwanaki masu zuwa Birtaniya za ta dakatar da fitar da abubuwan fasaha da kuma kayayyakin tace man fetur

7.Za a ƙayyade yawan kuɗaɗen da ƴan Rasha za su iya saka wa a asusun bankunan Birtaniya

8.Ya ce akwai yiwuwar a cire Rasha daga tsarin aika kuɗaɗe na ƙasashen yamma

9.Irin wannan mataki zai shafi Belarus a kan rawar da take takawa kan yaƙar Ukraine da ake yi

10.Birtaniya za ta gabatar da dokar aikata miyagun laifuka da suka shafi harkokin kuɗaɗe gaban majalisa kafin a tafi hutun Ista.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here