‘Yan Najeriya na Cikin Talauci Saboda ba Kowa ya Mallaki Sama da N500 a Rana ba – Farfesa Segun Ajibola
Wani Farfesan Tattalin arziki ya bayyana matsayar Naira game da karfin darajarta.
A bayaninsa, Yan Najeriya na cikin talauci saboda ba kowa ya mallaki sama da N500 a rana ba.
Farfesa yace a nan gida N500 zata kosar da mutum, amma a waje ba ta da daraja.
Abuja – Tsohon shugaban kwalejin ma’aikatan bankin Najeriya (CIBN), Prof Segun Ajibola, ya bayyana cewa mutane su daina ruduwa da fadin darajar Naira idan aka danganata ga Dalar Amurka.
Segun ya bayyana cewa da N500, dan Najeriya zai ci ya koshi a yau.
Farfesan wanda Malamin ilmin tattalin arziki ne a jami’ar Babcock, ya bayyana hakan ne ranar Laraba, 22 ga Satumba, yayin hira a tashar NTA.
A cewarsa, darajar kudi na nuni ga karfin tattalin arzikin kasa da kuma rauninsa.
Yace:
Read Also:
“Har yanzu Naira na da karfi. Da N500, dan Najeriya zai iya ciyar da kansa a yau amma idan muka danganata a Dalar Amurka ko Fam, babu abinda zaka iya yi da Fam daya a Landan, ba zaka iya sayan wani abun kirki da Dala daya ba a New York (Amurka).”
“Saboda haka, akwai banbanci tsakanin darajar Naira a Najeriya da kuma darajarta a waje, idan akayi la’akari da abinda mutum zai iya saya da shi.”
“Mun lura cewa Naira a yanzu na da darajar a Najeriya amma a kasar waje, akwai matsala.”
Amma fa N500 ba zai kosar da mutum guda a rana ba
A wata hira daban kuma da jaridar Guardian, masani tattalin arzikin ya yi fashin baki kan maganarsa inda yace N500 zai ciyar da mutum sau daya ba a rana guda ba.
A cewarsa, yanzu sai mutum ya tanadi N45,000 a wata yaci abinda yake so a Najeriya kuma hakan yasa talauci ya yawaita.
Yace:
“Abin shine:
A N500 sau daya, N1500 kullum, N45,000 a wata, kudin da dan Najeriya ke da shi ba zai isa ciyar da shi ba kuma hakan ke haifar da yawaitar talauci.”