Takar Dakon Man Fetur ta ƙone a Adamawa

 

Rahotanni daga Yola, babban birnin jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa gobara ta tashi a lokacin da wata tankar dakon man fetur ke sauke mai a wani gidan mai da ke birnin, sai dai lamarin bai kai ga asarar rai ba.

Gobarar ta faru ne a kan titin Numan kusa da filin jirgin sama na jihar Adamawa.

Zuwa yanzu ba a gano musabbabin gobarar ba sai dai lamarin ya janyo fargaba da ya kai ga dandazon mutane sun toshe hanyar shiga birnin.

An kuma tura jam’ian tsaro wurin domin kare mutane da kuma hana su zuwa ɗibar man.

Wannan ibtila’i na gobara ko faɗuwar tankar mai na cigaba da zama babbar matsala a Najeriya inda ko a ranar 18 ga watan Janairun wannan shekarar, aƙalla mutane 86 suka mutu yayin da wasu 55 suka jikkata a lokacin da suke ɗibar mai bayan fauwar wata tankar mai.

Ko a bara ma an samu haɗurran tankar dakon man fetur da ya yi sanadiyyar mutuwar ɗaruruwan mutane da kuma asarar dukiya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here