Tankin Ruwa ya yi Sanadiyyar Kashe Mutane 2 a Jihar Legas
Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa ta bayyana yadda wani iflia’i ya fado wa wasu mazauna jihar Legas.
Mutum biyu sun mutu yayin da uku suka raunata lokacin da tankin ruwa ya fado kan wani gida da ke gefe.
Ana yawan samun irin wadannan lamurra na faduwar gini ko makamancinsa a birnin Legas, Kudu maso Yamma.
Bariga, jihar Legas – Rahoton da muke samu daga jihar Legas na bayyana cewa, wani tankin ruwa ya fado ya danne wasu mutane a jihar Legas, inji jaridar The Nation.
Read Also:
Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ce ta bayyana hakan, inda tace tankin ya danne mutanen biyu ne Ladi Lak da ke Bariga jihar Legas a daren Lahadi 21 ga watan Agusta.
Kodinetan shiyyar Kudu maso Yamma na hukumar NEMA, Ibrahim Farinloye ya tabbatar wa namema labarai faruwar lamarin, inji Daily Nigerian.
Da yake bayani, Farinloye ya ce tankin ruwan wani bene mai hawa biyu ne ya fado kan wani gidan kasa da ke kusa dashi, ya kashe namiji babba da karamin yaro, kana ya raunata mutane uku.
A cewarsa, shugabanni a yankin Bariga ne suka kai mutanen da suka samu raunuka ga asibiti kafin zuwan jami’an hukumar agajin gaggawa.