Starlink: Tankiya ta Kaure Tsakanin Musk da Gwamnatin Afrika ta Kudu

 

Takun saƙar da ake yi tsakanin shugaban kamfanin Starlink Elon Musk da gwamnatin Afirka ta Kudu kan gazawar kamfanin wurin fara aiki a ƙasar ya samo asali ne daga dokokin ƙarfafa baƙar fata na ƙasar, kuma yana iya kasancewa ɗaya daga cikin dalilan da ke haifar da taƙaddamar diflomasiyya tsakaninta da Amurka.

A wani saƙo da wallafa a shafinsa na X, Mista Musk ya yi zargin cewa ba a ba shi damar ƙaddamar da ayyukan kamfanin a ƙasar ba saboda shi ba baƙin fata ba ne.

Sai dai hukumar sadarwa mai zaman kanta ta Afirka ta Kudu (Icasa) – wanda ita ce hukumar da ke kula da harkokin sadarwa da watsa shirye-shirye – ta shaida wa BBC cewa Starlink bai taɓa miƙa buƙatar neman lasisi ba.

A ɓangaren ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, ta ce ana maraba da kamfanin ya yi aiki a ƙasar “idan har ya bi dokokin cikin gida”.

Kafin ya samu damar aiki a Afirka ta Kudu, Starlink yana buƙatar samun lasisi, wanda ke buƙatar cewa sai ya samu mallakar kashi 30% daga mutanen da suka fito daga al’ummomin da aka bayyana a matsayin marasa galihu.

Hakan dai na nufin yawancin baƙaƙen fata a Afirka ta Kudu, waɗanda aka haramtawa shiga al’amuran da suka shafi tattalin arziki a zamanin tsarin wariyar.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here