An Fara Tantance Matasan da  Za’a Dauka Aikin ‘Yan Sanda

 

Gwamnatin Kaduna ta sanar da cewa ta fara tantance matasan da za’a dauka ‘yan sandan jaha domin tabbatar da tsaro jahar.

Kwamishina kananan hukumomi a Kaduna, Ja’afaru Sani, ya ce tantance matasan shine mataki na farko wajen samar da ‘yan sandan jihar.

Sanata Uba Sani ya ce ya na aiki a kan kudirin da zai bayar da damar samun ‘yan sandan tarayya da na jihohi.

Gwamnatin Kaduna ta fara tantance matasa a kokarinta na shirin fara aiki da ‘yan sandan jiha domin inganta tsaro a jihar, kamar yadda TheCable ta rawaito.

Uba Sani, Sanata mai wakiltar jihar Kaduna ta tsakiya, shine ya sanar da hakan jim kadan bayan kammala wani taro da ma su ruwa da tsaki a sha’anin tsaro.

Taron ya samu halartar ‘yan majalisar jiha da na tarraya daga Kaduna, shugabannin kananan hukumomi 15 da ke arewacin Kaduna, da hakimai.

Da ya ke magana da manema labarai bayan kammala taron, Sanata Sani ya bayyana cewa ya na aiki a kan kudirin neman sake fasalin ‘yan sanda domin fuskantar kalubalen tsaro da kasa ke fama da shi.

A cewarsa, idan kudirin ya samu karbuwa a majalisa, za’a kirkiri ‘yan sandan jaha.

“Ina aiki a kan wani kudiri da zai sauya fasalin aiki da kunshin rundunar ‘yan sanda, hakan zai bayar da damar samun ‘yan sandan jiha da na tarayya.

“Mu na son kawo karshen kalubalen tsaro a jihar Kaduna da Nigeria baki daya.

“Za mu yi aiki da jama’a wajen magance matsalar tsaro a jiha, ta hanyar aiki kafada da kafada da sarakunan gargajiya da sauran shugabannin siyasa.

Gwamnan jiharmu a shirye ya ke tsaf domin kawo karshen matsalar tsaro,” a cewar Uba Sani.

A nasa bangaren, kwamishinan kananan hukumomin jihar Kaduna, Ja’afaru Sani, ya ce tantance matasan shine mataki na farko wajen samar da ‘yan sandan jiha.

A cikin watan Mayu na shekarar 2019 ne babba sifeton rundunar ‘yan sanda, Mohammed Adamu, ya sanar da cewa shugaba Buhari ya bashi izinin fara tsara hanyoyin samar da ‘yan sandan jiha a fadin Nigeria.

A cikin watan Agusta, gwamnatin tarayya ta amince da fitar da biliyan N13.3 domin kaddamar da tsarin ‘yan sandan jihohi a Nigeria.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here