Tanzania ta Haramta Amfani da Sanannen Littafin Yara a Makarantu Saboda Zargin Kare ‘Yancin Masu Neman Jinsi Daya
Gwamnatin Tanzania ta haramta amfani da sanannen littafin yaran nan mai suna Diary of Wimpy Kid wajen koyarwa a makarantun kasar saboda zargin kare ‘yancin masu neman jinsi daya.
Littafin yana da mujalladi da dama, kuma daga cikinsu yanzu gwamnatin ta haramta guda 16.
Ministan ilimi na kasar Farfesa Adolf Mkenda ya ce littafin yana jefa ilimin yara cikin hadari kuma ya saba da al’adun Tanzania.
Read Also:
Makenda ya bukaci iyaye da su rika duba jakar makaranta ta yaransu akai-akai domin su tabbatar ba sa dauke da wadannan littattafai.
Duk wata makaranta da ta ci gaba da amfani da jerin littattafan za ta fuskanci hukunci na ladabtarwa da kuma kotu, ciki har da soke rijistarta.
Wadanda aka haramta sun hada da;
Diary of a Wimpy Kid: Rodrick Rules
Diary of a Wimpy Kid: The Last Straw,
Diary of a Wimpy Kid: The Ugly Truth
Diary of a Wimpy Kid: Cabin Fever.
Diary of a Wimpy Kid: The Third Wheel
Diary of a Wimpy Kid: Hard Luck
Diary of a Wimpy Kid: The Long Haul
Diary of a Wimpy Kid: Old School
Diary of a Wimpy Kid: Double Down
Diary of a Wimpy Kid: The Gateway.