Gwamnatin Jihar Taraba ta Zabtare Kuɗin Jami’a da Kaso 50 ta Maida Makarantun Firamare da Sakandire Kyauta

 

Gwamnan Taraba, Agbu Kefas, ya maida ilimin makarantun Firamare da sakandire kyauta ga ‘yan jihar.

Ya ce wannan na ɗaya daga cikin alkawurran da ya ɗauka lokacin kamfe, bayan haka zai rage raɗafin cire tallafin man fetur.

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan gwamna Kefas ya zabtare kuɗin jami’a da kaso 50, lamarin da ɗalibai suka yi maraba da shi.

Taraba state – Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba da ke Arewa Maso Gabashin Najeriya ya maida karatun makarantar Firamare da Sakandire kyauta a jihar, in ji rahoton Daily Trust.

Gwamna Kefas ya bayyana wannan kyakkyawan labari ga dalibai da iyaye yayin da ya kai ziyara makarantar Firamare da ke Wukari ranar Jumu’a, 7 ga watan Yuli, 2023.

A cewar mai girma gwamnan, daga zangon karatu mai zuwa, karatu a makarantun Firamare da Sakandire ya koma kyauta a faɗin jihar Taraba.

Gwamna Kefas ya jaddada cewa gwamnati ya kamata a ce ta ɗauke duk wasu kashe-kashen kuɗi a makarantun, bai kamata a bar ɗalibai da wahalar biyan kuɗi ba.

Meyasa gwamnan ya maida ilimi kyauta a Taraba?

Agbu Kefas ya kara da cewa ya maida ilimin Firamare da Sakandire kyauta ne domin cika alƙawarin da ya ɗaukar wa al’ummar Taraba lokacin yaƙin neman zaɓe.

Ya ce baya ga cika alkawari, ya yi haka ne domim rage wa mutane raɗaɗi da wahalhalun rayuwa waɗanda suka biyo bayan cire tallafin man fetur a Najeriya.

Gwamnan ya zabtare kuɗin jami’a da kaso 50

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa gwamnan ya maida ilimi kyauta kwanaki kaɗan bayan ya zabtare kuɗin jami’a da ɗalibai ke biya da kaso 50 cikin ɗari domin rage radaɗin da ake fama.

Mafi yawan ɗaliban jami’a mallakin gwamnatin jihar Taraba sun yi murna da farin cikin wannan ragi. A cewarsu rage kuɗin zai taimaka wa rayuwarsu, kamar yadda Guardian ta ruwaito.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here