Kadan Daga Cikin Tarihin Marigayi Dr. Mahmud Tukur
A ranar Juma’a, 9 ga watan Afrilu, 2021, Dr. Mahmud Tukur ya rasu bayan gajerar rashin lafiya a garin Abuja.
Tun a ranar aka birne shi a Yola, jahar Adamawa. Wannan karo, legit.ng Hausa ta tattaro maku kadan daga cikin tarihin Marigayi Mahmud Tukur.
1. Haihuwa
An haifi Mahmud Tukur ne a shekarar 1939 a garin Yola, jahar Adamawa. Marigayin ya rasu kenan ya na da shekara 82 a Duniya.
Cikin ‘yanuwan Tukur na jini akwai Injiniya Hamman Tukur da ya yi aiki a Kad Poly, NEPA da RMFAC da kuma babban ‘dan siyasa Alhaji Bamanga Tukur.
2. Karatu
Bayan karatun firamare da sakandare a gida, Marigayin ya tafi wata jami’a a kasar Wales ya samu digirinsa a fannin ilmin siyasa da harkokin kasar waje.
Daga baya Tukur ya tafi jami’ar Pittsburg da ke kasar Amurka ya yi digirinsa na biyu a kan ilmin harkokin kasar waje.
Read Also:
Bayan nan ya dawo fitacciyar jami’ar nan ta gida, Ahmadu Bello da ke Zariya, ya yi digiri na uku watau PhD.
3. Aiki
Marigayin ya yi aiki a jami’ar Ahmadu Bello har ya zama Darekta a tsangayar koyar da aikin gwamnati.
Daga nan ya tafi makarantar Abdullahi Bayero ta Kano a 1975, bayan ta zama jami’a, ya zama shugabanta na farko a 1977.
Tukur shi ne shugaban kamfanin Fukarabe Industries Ltd, kuma darekta a kamfanin Cadbury, sannan shi ya ke kula da Policy Analysis Ltd.
4. Shiga gwamnati
Tukur ya yi aiki a kwamitin da Adebo da Udoji su ka jagoranta wajen karin albashi a gwamnatin tarayya a 1976.
Bayan nan, Tukur ya na cikin wadanda su ka sa hannu wajen tsara kundin tsarin mulki na 1976 da 1996 da shirin Vision 2010 na 1997.
A 1984 ne aka nada Mahmud Tukur a matsayin Ministan sana’o’i da masana’anta, bayan ‘yan watanni a kan mulki ya bar kan karaga.
5. Rubuce-rubuce
Marigayin ya rubuta littafin “Leadership and governance in Nigeria : The Relevance of Values” a shekarar 1999.