Takaitaccen Tarihin Rayuwar Muhammad Rabi’u Yusuf Takai

 

An Haifi Muhammad Rabi’u Yusuf Takai A Garin Kano Shekarar 1976 Muhaifinsa Wato Yusuf Takai Wanda Akewa Lakabi Da Sarki Ya Dawo Cikin Garin Kano Domin Aikin Gwamnati Inda Yake Zaune Da Iyalinsa A Unguwar Hausawa Sabontiti Dake Zooroad Kano.

TARIHIN YIN KARATU

Rabi’u Yusuf Ya Shiga Makarantar Islamiyya A Unguwar Gandun Albasa Kano A Shekarar 1982 Ya Kuma Gama A Shekarar 1988,Daga nan ya tafi makarantar gaba da firamare karamar sakandare wato Junior secondary school a sabuwar kofa anan garin Kano a shekarar 1989

Zuwa 1992 Daga Nan Kuma Ya Tsallaka Zuwa Makarantar Babbar Sakandare a unguwar sharada wadda ake kira gomman girama sakandare (government grammar secondary school sharada) inda ya kammala a shekarar 1994.

Bayan kammala sakandare Rabi’u ya kuma shiga makarantar kwalejin share fagen shiga jami’a wato CAS daga wannan karatu ya samu sahalewar shiga jami’ar Bayero a bangaren karatun lauya a wajejen Shekarar 1996/1997 ya kuma kammala a shekarar 2002 bayan kammalawa sai kuma ya zarce zuwa ga Makarantar Horon aikin lauyoyi da take enugu wato Nigerian law school inda yazama cikin dalibai na farko da suka fara ta,bayan kammalawa ya kuma tafi zuwa bautar ƙasa a garin abia a kudancin Nigeria.

Sanna ya gama bautar ƙasa ya dawo gida ya samu rubuta jarabawar karshe ta tabtancewa domin zama cikakken lauya ya kuma samu nasara a inda ya zama cikakken lauya a shekarar 2004.

Fannin AIKI

Bayan Zaman Barrister Rabi’u Yusuf Takai Cikakken Lauya Ya Fara Aiki Matsayin Lauya Mai Zaman Kanshi Daga Baya Ya Shiga Aiki Tare Da Gomnatin Jaha (Lauyan Gomnati) Daga Cikin Gwagwarmayar Aiki Yayi Ayyuka A Gurare Daban-daban Kamar,Aiki A Hukumar Zakka Da Hubusi Ta Jahar Kano Inda Har Ya Kai Matsayin Sakatare Kuma Legal Adviser A Wannan Gurbi,Ya Kumayi Aiki A Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Ta Jahar Kano Inda Har Ya Kai Matsayin Shugaba (Head) A Ɓangaren (Unit) Na Anticorruption Prevention Unit,Sannan Ya Zama L.A Ma’ana Legal Adviser Ga DG Na Wannan Guri Kuma Na Wannan Lokaci Wato Malam Aminu Inuwa Har Ma Ya Rike Mana Acting DG Kuma A Lokacin Mulkin Gomna Malam Ibrahim Shekarau.

Daga Wannan guri Barrister Rabi’u Yusuf Takai Ya Dawo Ma’aikatan Shari’a Da Aiki,Inda Bayan Wani Dan Lokaci Kuma Ya Koma Zuwa Hukumar Nan Dai Ya Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Ya Kuma Zama Director Citizens Right Steal A Hukumar A Wannan Yanayi Ne Dai Mai Girma Ministan Shari’a Na Zamanin Shugaban Kasar Nijeriya Muhammadu Buhari Wato SAN.Abubakar Malami Ya Nemeshi Da Yazo Ya Bashi Gudunmawa A Tafiyarshi Ya Bashi Muƙamin Mataimaki Na Musamman Kan Abubuwan Da Suka Shafi Kwatowa Da Kuma Tsare Almundahana Da Dukiyar Al’umma (S.A Recovery And Management To Minister Of Justice).

Daga bisani Kuma Sai Mai Girma Shugaban Kasa Ya Nemi Ya Kasance Daya Daga Cikin Masu Bashi Shawara Inda Ya Bashi Muƙamin Mai Ba Da Shawara Na Musamman Kan Abinda Ya Shafi Shari’a Kan Tuhume-Tuhume (Prosecution Coordination) S.A “Akan Yanda Za’a Tsara Kuma A Tantance Aga An Dunkule Yanda Ake Gabatar Da Kara A Gaban Kotu”.

Kuma Yana Kan Wannan Matsayi Ya Samu Kira Da Matsawa Daga Al’ummar Yankinsa Na Takai Da Kuma Sumaila Akan Ya Fito Domin Wakiltarsu A Majalisar Wakilai Ta Goma.

NASARORIN

A Yanzu Haka Shi ne Shugaban Kwamitin Yarjejeniya Tsakanin Najeriya Da Ƙasashen Waje,A Zauren Majalisar Tarayya Ta Najeriya.

Kuma Hon. Rabiu Ibn Yusuf shine Zababben Sabon Dan Majalisar tarayya daga Jihar Kano wanda yafi kowa kawo Kudirori a Majalissa.

Kuma Shine Da Majalisar Da Ya Fara Hidimar Aiki Ga Yankinsa Daga Kwana Ashirin Na Rantsuwarsa.

Haka Kuma Barrister Shine Kaɗai Zaɓaɓɓen Da Majalisar Tarayya Sabo Wanda Ya Rabauta Da Shugabancin Kwamiti Guda

KARSHE

Daga Karshe Dai A Yanzu Barrister Rabi’u Yusuf Takai Shine Ɗan majalisar Tarayya Mai Wakiltar Kananan Hukumomin Takai Da Sumaila Dake Yankin Kano Ta Kudu A Jihar Kano Nijeriya.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here