Yawan Yin Taron ƙolin ƙasashen Yankin Tekun Guinea Zai Taimaka Wajen Samar da Zaman Lafiya – Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce yawan yin taron ƙolin ƙasashen yankin tekun Guinea zai taimaka wajen samar da zaman lafiya da inganta tsaron yankin.
Yayin da yake jawabin a taron shugabannin ƙasashen yankin tekun Guinea da ke gudana a Accra babban birnin ƙasar Ghana, shugaba Buhari ya jaddada cewa taron na da matuƙa muhimmanci wajen magance matsalolin da ke addabar yankin.
Ya ce ”Dole mu ƙarfafa tarukan ƙungiyar ƙasashen yankin tekun Guinea da na shugabannin ƙasashen yankin domin samun damar tattauna matsalolinmu”.
Read Also:
”Da kuma lalubo hanyoyin magance su, don samar da zaman lafiya, da tsaro da kuma ci gaban ƙasashen yankin tekun Guinea”, in ji Buhari.
Shugaban ya jaddada ƙoƙarin da Najeriya ta yi wajen yaƙar ayyukan masu fashin teku a yankin tekun Guinea, tare da kiran sauran ƙasashen ƙungiyar da su samar da dokoki da za su haramta fashin teku, kamar yadda Najeriya ta yi.
Shugaban na Najeriya ya yaba wa takwaransa na Ghana Nana Akufo-Addo, wanda ya jagoranci taro, bisa yadda ya jagoranci gudanar da taron.
Haka kuma shugaba Buhari ya yaba wa babbar sakatariyar ƙungiyar mai barin gado, Ambassador Florence Ukonga tare da sauran jagororin ƙungiyar kan sadaukarwar da ya ce sun yi wajen sauke nauyin da aka ɗora musu na jagorantar ƙungiyar.