Babu Wanda Zai Tayar da Hankalin ‘Yan Kudu a Arewa – Gwamnan Jahar Jigawa
Gwamnan Jigawa ya yi tsokaci kan tsangwamar da ake yiwa Fulani a kudancin Najeriya.
Badaru yace yan kudun dake Arewa su kwantar da hankalinsu, babu wanda zai taba su.
Gwamnan jahar Jigawa, Muhammad Badaru, ya kwantar hankalin yan kudancin Najeriya mazauna jaharsa cewa shirye yake da karesu rayukansu da dukiyoyinsu.
Gwamnan ya bada wannan tabbaci ne ranar Asabar yayinda ya karbi bakuncin gwamnan jahar Ebonyi, David Umahi, a jahar Jigawa, Premium Times ta ruwaito.
Read Also:
Gwamna Badaru ya gayyaci takwaransa na Ebonyi ne domin kaddamar da wani hanya a karamar hukumar Babura. Badaru ya yi amfani da daman domin jawabi ga Inyamuran da suka fita kwansu da kwarkwatansu domin tarban gwamnan na Ebonyi.
“Muna godiya mutan kudu na zaman lafiyansu a Jigawa tare da mu, kuma muna son bayyanawa kowa cewa ku kwantar da hankalinku a Jigawa da sauran jahohin Arewa,” Badaru yace
“Ku fadawa yan siyasan dake son kawo rashin jituwa kasar nan cewa ba zasuyi nasara ba saboda babu wanda zai tayar da hankalin yan kudu a Arewa.”
Gwamnan ya ce gwamnati ba zata zuba ido a cutar da wani a Jigawa ba.
A jawabinsa, Umahi ya godewa gwamnonin Arewa bisa kokarin samar da zaman lafiya a Najeriya.