Taƙaddama ta ɓarke a Majalisar Dattijai Tsakanin Sanatoci Biyu
Taƙaddama ta ɓarke a zaman majalisar dattijai na ranar Talata ya yin da aka kawo kudirin gina babbar cibiyar duba marasa lafiya ta ƙasa a karamar hukumar Mubi, jahar Adamawa.
Taƙaddamar ta fara ne daga lokacin da Sanata daga jahar Adamawa, Aishatu Binani ta kawo misalin cewa ƙaramar hukumar Mubi ta zarce jahar Bayelsa girma.
Sai dai misalin be ma Sanata Dickson daga jahar Bayelsa daɗi ba inda ya mike ya gargaɗe ta da tayi abinda ke gabanta ta daina saka jahar sa a ciki Taƙaddama ta ɓarke a majalisar dattijan ƙasar nan a zamanta na ranar Talata lokacin da sanata Aishatu Binani ta jam’iyyar APC daga Adamawa ta bada misalin jahar Bayelsa a cikin jahohi marasa yawa.
Read Also:
Sanata Binani ta kawo wannan maganar ne ya yin da take ƙoƙarin kare kudirin data kai gaban majalisar kan buƙatar a gina cibiyar duba marasa lafiya a karamar hukumar Mubi, Adamawa.
Binani ta bayyana ma majalisar cewa, Mubi na da faɗin ƙasa da takai kimanin 506.2km2 wanda a cewarta karamar hukumar ta zarce jahar Bayelsa girma.
Ta kuma ƙara da cewa jahar Bayelsa ɗake da kananan hukumomi bakwai na da yawan jama’a kimanin 1,704,515. Sai dai jawabin nata bai ma Sanata Seriake Dickson na jam’iyyar PDP daga Bayelsa dadi ba inda ya mike ya ƙaryata zancen nata.
Sanata Dickson ya ce girman jahar Bayelsa (wanda ya haɗa da faɗin kasa da kuma na ruwa) ya ninka girman wasu jahohin ƙasar nan sau uku.
Sanatan ya kuma gargaɗi Binani da ta gabatar da kudirinta ba tare da ta kawo misali da jahar Bayelsa ba, kamar yadda jaridar Dailytrust ta ruwaito.
Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan ya katse taƙaddamar sanatocin biyu inda ya gargaɗi Sanata Dickson da ya daina kawo abubuwan da basu da alaƙa da kudirin.
Daga ƙarshe kudirin na Aishatu Binani ya tsallake karatu na farko bayan gudanar da zaɓe akansa.