Shugaba Tinubu ya ba da Umarnin a Gudanar da Bincike Kan Harin Bom a Kaduna
Shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu ya ba da umarnin a gudanar da cikakken bincike kan harin bom da rundunar sojin ƙasar ta ce ta kai bisa ‘kuskure’ a jihar Kaduna.
Read Also:
Shugaban ya bayyana haka ne yayin miƙa saƙon ta’aziyya ga al’ummar jihar Kaduna da kuma alhini ga mutanen da suka ji rauni sakamakon lamarin da ya faru a ƙauyen Tudun Biri a ƙaramar hukumar Igabi.
Cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan kafafen yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya fitar, Shugaban Najeriyar ya ce abin takaici ne inda kuma ya bayyana jimami kan asarar rayukan da aka yi.
Shugaban Najeriyar ya kuma buƙaci mutane su kwantar da hankalinsu yayin da hukumomi ke nazari a kan lamarin.
Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin a bai wa mutanen da suka jikkata kulawa sosai a asibiti tare da addu’ar Allah ya ji ƙan waɗanda suka rasu.