Shugaba Tinubu ya Buƙaci a Gudanar da Bincike Kan Yawan Hatsarin Jirgin Ruwa a Fadin Najeriya

 

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya jajanta wa iyalan waɗanda hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su a ƙaramar hukumar Mokwa ta jihar Neja da kauyen Gurin da ke karamar hukumar Fufore ta jihar Adamawa.

Waɗannan haɗurran sun yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, ciki har da yara.

Shugaban ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga al’ummomin da abin ya faru gare su tare da neman a kai musu ɗauki cikin gaggawa.

Tinubu ya kuma buƙaci a gudanar da cikakken bincike kan yawan hatsarin jirgin ruwa da ake samu a ƙasar.

Ya umurci hukumomin gwamnati daban-daban da suka hada da jami’an tsaro da sojojin ruwa da hukumomin kula da harkokin sufuri, da su hada kai sosai wajen gano musabbabin wadannan bala’o’i na hatsarin jirgin ruwa da za a iya kiyayewa.

Shugaban ya jaddada kudirinsa na ganin ya dauki nauyin hukumomin gwamnati kan duk wata matsala ta tsaro ko rashin tsaro.

Ya bayar da umarnin sake duba matakan tsaro da tsaurara dokokin da ake da su na tafiyar da ayyukan jiragen ruwa a fadin kasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com