Tinubu ‘Dan Takarar da ya Cika Abin da Ake Bukata – Shettima
Tsohon gwamnan Borno, kuma abokin Bola Ahmad Tinubu na APC, Kashim Shettima ya bayyana kadan daga dabi’un abokin takararsa.
Shettima ya ce Najeriya na bukatar shugaba mai dabi’u uku daga shugabannin Najeriya don iya rike kasar da kyau.
Gwamnan jihar Legas ya amince da batun Shettima, ya ce Tinubu ne ya cancanci gaje kujerar shugaba Buhari.
Ikoyi, Legas – Abokin takarar Tinubu a zaben 2023, Kashim Shettima ya bayyana abubuwan da kasar nan ke bukata daga shugaban da zai gaji Buhari a 2023 don kawo ci gaba a Najeriya, Punch ta ruwaito.
Da yake magana ranar Alhamis 15 ga watan Satumba bikin murna na 96 na kungiyar Yoruba Tennis Club da aka yi a Ikoyi ta Legas, Shettima ya ce Tinubu dan takarar da ya cika abin da ake bukata.
Read Also:
A cewar Shettima, Bola Ahmad Tinubu na jam’iyyar APC ne ya cika duk wasu abubuwan da ake bukata daga shugaban da ya cancanci hawa kujerar mulkin Najeriya.
Ya kuma ce, Tinubu da karimci irin na tsohon shugaban Najeriya Sani Abacha da kuma jajircewa kamar na shugaban Najeriya na yanzu, Manjo Muhammadu Buhari mai ritaya.
Tinubu na da hali irin na Obasanjo, inji Shettima
Baya ga wadannan, ya ce Tinubu na da tsarin aiki irin na tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, rahoton TheCable.
A cewarsa:
“A ‘yan kwanakin nan, mun ga yadda abubuwa ke dagulewa game da rashin yarda da ra’ayin hadin kan kasa. Gaskiyar magana ita ce, gina kasa aiki ne da ya kamata ya ci gaba, kuma dole ne mu ci gaba da kyautata zaton samun haka.”
Hakazalika, gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu yace tabbas Tinubu ne dan takarar da ya cancanci ci gaba da aiki daga inda shugaba Buhari ya tsaya.