Jam’iyyar APC ta yi Kira ga Shugaba Tinubu da ya Saka Dokar Ta-ɓaci a Jihar Ribas

 

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta sake yin kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sanya dokar ta-ɓaci a jihar Ribas saboda rikicin siyasar da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a cewarta.

Jam’iyyar ta buƙaci da a tura sojoji da makamai a girke su a wuare na musamman a jihar domin kare abin da ta kira ɓarkewar rikici.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa shugaban riƙo na jam’iyyar a jihar, Chief Tony Okocha, shi ne ya yi kiran a yau Laraba a wani taron manema labarai a babban birnin jihar, Port Harcourt, yana mai cewa akwai lamau ƙarara na rashin bin doka da oda a jihar, wanda ya ce wasu da ba hukuma ba suna shiryawa.

Kuma ya ce idan ba a gaggauta ɗaukar matakin dakatar da yanayin ba, za a makara.

Mista Okocha ya bayyana cewa dokar nan mai cike da taƙaddama ( Law No 2 of 2024 ), wadda ƴan majalisar dokokin jihar masu biyayya ga ministan Abuja suka yi, ba sun yi ta ba ne da nufin tsawaita wa’adin shugabannin ƙananan hukumomin jihar da wa’adinsu ya ƙare ba, ya ce an yi ta ne saboda gaba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here