Shugaba Tinubu Ya Gabatar wa da Kotu Shaidar Karatunsa na Jami’ar Chicago
Shugaba Tinubu ya kare kansa game da rudanin da ya dabaibaye batun karatunsa a gaban Kotun sauraron korafin zaɓe mai zama a Abuja.
Ta hannun lauyansa, shugaban kasan ya gabatar da takardun karatun da ya yi a jami’ar Chicago da ke ƙasar Amurka ranar Talata.
Wannan na zuwa ne yayin da Tinubu ya buɗe fagen kare kansa game da korafin PDP da Atiku Abubakar.
FCT Abuja – Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gabatar kwafin takardun karatunsa na jami’ar jihar Chicago ta ƙasar Amurka a gaban kotun zaɓe mai zama a Abuja.
Shugaba Tinubu ya gabatar da takardun ne a matsayin shaidar tabbatar da karatunsa a gaban kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen shugaban ƙasa ranar Talata, 4 ga watan Yuli.
The Nation ta rahoto cewa Tinubu ya fara kokarin kare kansa kan ƙarar da PDP da ɗan takararta na shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar suka shigar
Read Also:
Bola Tinubu ya gabatar da takardun ta hannun lauyansa, Chief Wole Olanipekun, tare da takardar da ya karɓa daga hannun ofishin jakadancin Amurka a Najeriya tun a shekarar 2007.
Takardar dai ta wanke Bola Tinubu daga zargin aikata kowane laifi a ƙasar Amurka, ya kuma gabatar da takardar da hukumar ‘yan sandan Najeriya ta aike wa ofishin jakadancin Amurka don neman karin haske.
Tinubu ya gabatar da takardu 12 a gaban Kotun, wanda ya ƙunshi masu ɗauke da bayanan karatun da ya yi a jami’ar Chicago, waɗanda jami’ar ta ƙara tabbatar da sahihancinsu ranar 28 ga watan Yuni, 2023.
Sauran takardun da Tinubu ya gabatar a matsayin shaida
Bugu da ƙari, wanda ake ƙara ya gabatar da wasu kwafin takardu shida dangane da shige da fice da bayanan bizar tafiya-tafiyen Tinubu zuwa Amurka tsakanin 2011 zuwa 2021.
Idan baku manta ba a lokacin kamfe, tsagin adawa sun yi musun cewa shugaba Tinubu bai da shaidar karatu a jami’ar Chicago kamar yadda yake iƙirari.
Haka nan Atiku da PDP sun kafa hujja da wannan dalilin suka roƙi Kotu ta rushe nasarar da ya samu a zaben 25 ga watan Fabrairu, 2023.