Cire Tallafin Fetur: Gwamna Zulum ya Samar da Motoci 300 Domin Kai Manoma Gonakinsu

 

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya nemar wa manoman jihar hanyar zuwa gonakinsu cikin sauƙi.

Gwamnan ya samar da motoci 300 da za su yi jigilar sama da manoma 10,000 zuwa gonakinsu a lokacin damina.

Zulum ya ce an samar da motocin ne domin rage raɗaɗin da manoman su ke ji a dalilin tsige tallafin man fetur da aka yi a ƙasar nan.

Jihar Borno – Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, a ranar Talata ya samar da motoci 300 da za su riƙa jigilar sama da manoma 10,000 zuwa gonakinsu a ƙaramar hukumar Damboa.

Hakan na zuwa ne bayan ƴan ta’addan Boko Haram sun kai mabambantan hare-hare har guda biyu a ƙaramar hukumar satin da ya gabata.

Gwamnan wanda ya duba hanyar kafin zuwan manoman, ya tsaya domin tattaunawa da sojoji kan yadda jigilar manoman za ta tafi yadda ake so, jaridar Daily Trust ta yi rahoto.

Motocin za su kawo sauƙi ga manoma, Zulum

Ya kuma ƙara da cewa motocin za su rage raɗaɗin cire tallafin man fetur da aka yi ga manoman, rahoton NTA ya tabbatar.

A kalamansa:

“Domin rage raɗaɗin da manoma su ke ciki, gwamnatin jiha ta yanke shawarar samar da motocin da za su riƙa kai manoma gonakinsu ba tare da ko sisi ba a lokacin wannan daminar.”

“A nan wannan babban titin hanyar Maiduguri -Damboa, an samar da motoci 15 da motocin haya 30 domin samar da hanyoyin samun kuɗin shiga ga ƙungiyoyin sufuri na jiha. A jimlace motoci 60 za a samar a wannan hanyar domin kai manoman gonakinsu.”

“Ina roƙon manoman da su bayar da cikakken goyon baya ga sojojin Najeriya, suna wajen nan ne domin su kare ku da samar da tsari wanda zai tabbatar da an yi jigilarku cikin tsanaki.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here