Tinubu Zai Gabatar da Shettima Matsayin Mataimakinsa
Tinubu zai gabatar da Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa
Dan takarar shugaban Najeriya na jam’iyyar APC mai mulkin kasar, Bola Tinubu, zai gabatar da tsohon gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima ga ‘yan kasar a matsayin mataimakinsa a zaben 2023.
Wata sanarwa da jam’iyyar APC ta wallafa a shafinta na Tuwita ranar Talata da safe ta ce za a gabatar da Sanata Shettima ne ranar Laraba.
“A hukumance jam’iyyar APC za ta gabatar da dan takarar mataimakin shugaban kasarta, Sanata Kashim Shettima, ga al’ummar Najeriya ranar Laraba, 20 ga watan Yulin 2022,” a cewar sanarwar.
Read Also:
Za a yi bikin gabatar da shi ne a babban dakin taro na Shehu Musa Yar’Adua da ke Abuja da misalin karfe 11 na safe.
A makon jiya ne Bola Tinubu ya sanar da zaben tsohon Gwamnan Jihar Borno kuma Sanata mai wakiltar tsakiyar Borno, Kashim Shettima, a matsayin wanda zai yi masa mataimaki a zaben 2023.
Sai dai batun ya jawo muhawara mai zafi inda wasu ke ganin bai dace Tinubu, wanda Musulmi ne daga kudancin Najeriya, ya zabi Shettima, wanda Musulmi ne daga Arewacin kasar a matsayin mataimakinsa ba.
Amma jam’iyyar APC da ma Tinubu sun ce zabensa ba shi da alaka da addini.
Shettima gogaggen ɗan siyasa ne wanda ya daɗe yana jan zarensa a siyasa musamman a arewa maso gabas.
An haife tsohon ma’aikacin bankin a ranar 2 ga watan Satumbar 1966 kuma ya yi karatu a Jami’ar Maiduguri da kuma Jami’ar Ibadan.