SERAP ta Bukaci Shugaba Tinubu da ya Hana Ministocinsa, Tsoffin Gwamnoni Karbar Kudin Fansho
SERAP ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya hana ministocinsa, wadanda suka kasance tsoffin gwamnoni, karbar kudin fansho daga jihohinsu mabanbanta.
Kungiyar ta yi gargadi kan yiwuwar daukar matakin shari’a idan ministocin suka ci gaba da karbar kudaden fansho yayin da suke aiki a gwamnati mai ci.
Wadanda abun ya shafa sun hada da Nyesom Wike, Abubakar Badaru, Bello Matawalle, Gboyega Oyetola da sauransu.
Abuja – Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam Da kuma tabbatar da adalci a hukumomi da Ma’aikatun gwamnati (SERAP), ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya dakatar da ministocinsa, wadanda suka kasance tsoffin gwamnoni daga karbar kudin fansho daga jihohinsu.
Kungiyar mai zaman kanta ta yi kiran ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, 20 ga watan Agusta.
Read Also:
A cikin sanarwa da ta saki wanda Legit.ng ta gani, SERAP ta yi barazanar maka shugaban kasar na Najeriya a gaban kotu idan ya gaza dakatar da ministocin daga karbar fansho a matsayin tsoffin gwamnoni.
Jerin ministocin da abun yashafa
Nyesom Wike (jihar Rivers)
Abubakar Badaru (Jihar Jigawa)
Bello Matawalle (Jihar Zamfara)
Gboyega Oyetola (Jihar Osun)
David Umahi (jihar Ebonyi)
Simon Lalong (jihar Plateau)
Atiku Bagudu (jihar Kebbi)
Ibrahim Geidam (jihar Yobe)
Sanarwar ta ce:
“DA DUMI-DUMI: Mun bukaci shugaban kasa Tinubu da ya dakatar da tsoffin gwamnoni, Wike, Abubakar, Matawalle, Oyetola, Umahi, Lalong, Bagudu da Geidam daga karbar kudin fansho daga jihohinsu yayin da suke aiki a matsayin ministoci a gwamnatinsa, ko ya fuskanci mataki na shari’a.”
Jama’a sun yi martani
@rtsado01 ya yi martani:
“Matakin da ya dace.”
@Great_Bobb ya ce:
“Idan ba don rashin doka ba, me zai sa su ci gaba da karbar fansho?”
@Pa_Pa_Jay ya ce:
“Kun fara kuma ko.”
@Gokingvii
“Bata lokaci. Abun da kuke yi kawai shine shigar da kara. Ban taba ganin wani da ya fito da sakamako mai kyau ba.”