Shugaba Tinubu ya Sanya Hannu Kan Karin Kasafin Kudin 2023

 

Shugaban kasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kan karin kasafin kudin 2023 wanda yake kan naira triliyan 2.17

Tinubu ya rattaba hannu kan takardar kasafin kudin ne a yau Laraba, 8 ga watan Nuwamba a fadar Villa.

Hakan ya biyo bayan amincewar da ya samu daga majalisun tarayya bayan kasafin kudin ya tsallake karatu na uku.

Abuja – Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu a kan karin naira tiriliyan 2.17 na kasafin kudin 2023.

Kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto, Tinubu ya sanya hannun ne a ranar Laraba, 8 ga watan Nuwamba, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne majalisar dattawa da ta wakilai suka amince da karin kasafin kudin 2023 na N2.17trn bayan tsallake karatu na uku.

Kafin aiwatar da kudurin, majalisar dattawa ta amince da rahoton zaman da aka yi tsakanin majalisun biyu kan karin kasafin kudin 2023 kamar yadda shugaban kwamitin kasafin kudi, Sanata Solomon Olamilekan Adeola ya gabatar.

Kudirin ya yi hanzarin tsallake karatu a majalisun tarayya kamar yadda yan majalisar suka ce don amfani kasa ne.

Tinubu dai ya aika sako majalisa inda ya nemi ta amince da N2,176,791,286,033 a matsayin karin kasafin kudin 2023 don magance karin albashin ma’aikata, tsaro da sauransu, rahoton Channels TV.

Shugaban kasar ya kuma aike da tsarin kashe kudi na MTEF na 2024-2026 zuwa majalisun tarayya.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com