Shugaba Tinubu ya Nemi Amincewar Majalisar Don Karɓo Bashin Dala Biliyan 8.6
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya rubuta wa majalisun dokokin ƙasar biyu takardar neman amincewarsu don karɓo ƙarin bashin dala biliyan 8.6 da kuma euro miliyan 100, kimanin naira tiriliyan 7.1.
Domin gudanar da manyan ayyuka a ɓangarorin wutar lantarki da gina tituna da samar da ruwan sha da gina layin dogo da kuma ɓangaren lafiya.
Haka kuma shugaba Tinubu ya aike da ƙwarya-ƙwaryar kasafin birnin Abuja zuwa ga majalisar domin neman amincewarta.
A yau ne kuma shugaban ƙasar zai gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2024 ga haɗin gwiwar majalisun dokokin biyu, bayan da majalisar zartarwar ƙasar ta amince da kasafin wanda ya kai naira tiriliyan 27.5
Read Also:
Wannan na zuwa ne bayan da majalisar ta sake nazarin tsarin kashe kuɗaɗen gwamnati na matsaicin lokaci, wanda aka yi ƙiyasin canjin dala a kan naira 700, tare da ƙiyasta gangar mai a kan dala 73.96.
A ranar Litinin ne, ministan kasafin kuɗi da tsare-tsare na ƙasar, Sanata Atiku Bagudu ya shaida wa manema labarai cewa majalisar zartarwar ta sake nazarin tsarin kashe kuɗaɗen gwamnati na matsaicin lokaci da manufar harkokin kuɗi, inda ta amince da naira 750 a kan kowace dala, da kuma ƙiyasta gangar mai a kan dala 77.96.
A shekarun baya-bayan nan dai Najeriya ta dogara da karɓo bashi daga ƙetare domin gudanar da wasu manyan ayyuka.
A baya dai adadin kuɗin da ake in Najeriya bashi ya kai naira tiriliyan 87.3, kamar yadda ofishin kula da bashi na kasar ya bayyana.
Lamarin da ke nuni da cewa adadin ka iya kai wa naira tiriliyan 94.
Hakan na nufin bashin da ake bin ƙasar, ya ninka – kasafin kuɗin da shugaban ƙasar ke shirin gabatarwa a yau na naira tiriliyan 27.5 – fiye da sau uku.