Yawan Kuɗaɗen da Shugaba Tinubu ya Kashe a Kan Tafiye-Tafiye a Cikin Watanni Shida
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kashe naira biliyan 3.4 a kan tafiye-tafiyen cikin gida da kuma na ƙasashen waje a cikin watanni shida na farkon mulkinsa, a cewar rahotanni.
Hakan na nufin Shugaba Tinubu da jami’an gwamnatinsa sun zarce kasafin kuɗin naira biliyan 2.49 da aka ware wa tafiye-tafiyensu a 2023 da kashi 36, kamar yadda jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito.
Read Also:
Punch ta ce duk da yake shugaban ya gaji kasafin kuɗin ne na rabin karshen shekarar 2023, “ya kashe sama da abin da aka ware a gaba-ɗaya shekarar daga watan Yuni zuwa Disamban 2023”.
Rahoton wanda BBC ba ta tabbatar ba, ya zo ne kusan mako ɗaya bayan da Shugaba Tinubu ya zaftare yawan jami’ai da za a bari suna yi masa rakiya yayin tafiye-tafiyensa da kuma na sauran manyan jami’an gwamnatinsa zuwa ƙasashen waje da kuma a cikin gida.
Kafin haka, an soki lamirin shugaban kan makudan kuɗaɗen da yake kashewa wajen tafiye-tafiye waɗanda ƴan Najeriya suke ganin sun yi yawa.
Ɗaya daga cikin tafiye-tafiyen ita ce, wadda gwamnatin Tinubu ta ɗauki nauyin jami’ai sama da 400 domin zuwa taron sauyin yanayi na COP28 da aka a yi Dubai, inda aka yi ta sukarsa.