Shin Mai Yasa Shugaba Tinubu ya Kori Ministoci Biyar ?
Mai magana da yawun shugaban Najeriya, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa sallamar ministoci da shugaban nasa ya yi ya dogara ne ga irin kallon da yadda ƴan Najeriya ke yi wa ministocin.
A wata hira da gidan talbijin na ARISE TV, Onanuga ya ce Tinubu ya yi amfani da tunanin ƴan Najeriya ne.
“A lokacin da aka rantsar da ministocin, shugaban lallai ya shaida musu cewa yana ƙarfin ikon ɗauka da sallamar mutum aiki kuma ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin ya kori duk wani ministan da ya fahimci ba ya aikin da ya kamata.”
“An yi wani taro a watan Oktoban bara inda shugaba Tinubu ya nanata maganarsa cewa a koyaushe zai iya sallamar duk wanda ya ga ba ya yn aiki.”
Read Also:
Onanuga ya ƙara da cewa sallamar ministocin ba lallai na nufin cewa ba su yi abin da shugaba Tinubun yake tsammani daga gare su ba.
“Shugaba Tinubu ya yi amfani da abin da ƴan Najeriya ke tsammani daga wurinsu. Makonnin da suka gabata a lokacin taron majalisar zartarwa, Shugaban ya ƙalubalanci ministocin su je su shaida wa ƴan Najeriya abin da suka yi a tsawon shekara guda.”
Shugaba Tinubu dai ya fahimci cewa ƴan Najeriya ba su gamsu da riƙon ludayin da dama daga ministocinsa amma kuma yana da ƙwarin gwiwar cewa gwamnati na yin bakin ƙaƙarinta amma ministocin ba sa fitowa su shaida wa al’ummar ƙasa abin da gwamnatin ke yi.” In ji Onanuga.
A ranar Laraba ne dai shugaba Tinubu ya sanar da yin garambawul ga ministoci da ma’aikatun gwamnatinsa, inda ya sallami ministocin guda biyar sannan ya sake wa mutum 10 ma’aikatu tare da naɗa sabbi guda bakwai.